Da kyar da jibin goshi Alhaji Baba ya shawo kan matarsa har ta hakura da batun Saratu Albishir. A daren nan, ba ita ta samu barci ba sai wajen karfe uku. Ya bi ta da lallami da lallashi da kalamai masu kwantar da hankali, kafin ta amince da batunsa.
“Yanzu dai ni duk ba wannan ba, zan daukar miki alkawarin zuwa gobe idan Allah Ya kai mu, zan bayyana miki duk abin da ake ciki.”
Nan da nan ta sake harzuka, musamman da ta ji ya ce “…duk abin da ake ciki.”
“To, me zai hana ka fada mini komai yanzu? Tsoron me kake ji? Kana zaton zan iya daurewa har zuwa safiya? Ba ka zaton cutar da ni kake yi a yanzu haka…?”
“Don Allah ki dakata.” Ya tarbi numfashinta, ya dakile ta daga wadannan mabambantan tambayoyi da take antaya masa. Al’amuran duk sun hargiste. Ya shiga mamakin yadda matarsa duk ta kidime, abin da yake ganin karami ne amma tana son mayar da shi na tashin hankali.
“Kin san dai ba zan cutar da ke ba. Duk tsawon rayuwarmu ta aure da ke, ina zaton ke ce mutum ta farko a duniyar nan da za ki iya shaidata, cewa ba zan iya cutar da ke daidai da dakika daya ba. To, me zai hana ki yi mini uzuri? Koma dai mene ne, ai tun da kika ga na boye miki shi, akwai dalili. Kuma kada ki fitar da zaton cewa dalilin nan an sakaya shi ne domin dadada miki ba munana miki ba.” Ya dauki lokaci yana magana, ita kuwa ta yi kasake tana saurarensa.
“Wannan ita ce maganata ta karshe da kai. Idan dai har ka san akwai batuna a cikin al’amarin nan, to ka sanar da ni yanzu. Idan kuma ka kiya, to na tabbata zan dauki sabuwar ma’ana a game da zamana da kai.”
“Ni dai ina hada ki da Allah, ki yi hakuri, insha Allah koma dai mene ne, zan bayyana miki shi zuwa gobe. Ki yi hakuri don girman Allah da Ya hada mu aure da ke har muka samu zuriya. Ni dai na gaya miki, babu abin da zan yi da nufin cutar da ke. Haba FATA, sanyin ruhina!”
Abin da ya fada ke nan, wanda hakan ya sanya wani murmushi ya bayyana a fuskarta.
A daidai lokacin da Farida ke murmushi, sai ta jiwo muryar ’yarta ta farka, tana kiranta. Nan da nan ta mike ta nufi dakin yara, inda ta samu yarinyar a farke. Nan ta gane cewa ashe fitsari ne ya matsa mata, don haka ta dora ta kan Fo. Bayan ta gama fitsarin, ta kintsa ta, ta sake shimfidar da ita, sai barci.