Uwargida Farida ta dade ba ta yi barci ba. Talatainin dare ne amma ta yi wa rufin daki kuri, babu abin da ke kai-komo a zuciyarta sai tunani da zullumi. Ba wani abu yake dugunzuma mata rai ba, illa abin takaicin da ya shigo mata gida.
“Abin takaici mana!” Abin da ta fada ke nan, bayan ta ja wani dogon numfashi. Duk tsawon zaman da take da mijinta, daidai da rana daya ba ta taba samun shaidar yana soyayya da wata ba sai wannan lokaci. Akwai dai lokutan da wata abokiyar wasansa ta yi ta cuso kai, tana nuna masa kauna, amma ta fake da cewa wasa take. Wannan lokacin sai da aka kai ruwa rana sannan ta yakice al’amarin. Idan da ba haka ba, ta tabbata cewa lallai da an yi mata sakiyar da ba ruwa.
“Kuma ni ba batun kin kishiya nake ba, domin kuwa kamar yadda Musulunci ya tsara, ai alheri ne.” Ta ci gaba da tunani, amma bakinta yana mui-mui, sautukan kalmomin na fitowa, ba tare da ta ankara ba. “Babban abin gudu shi ne, mutum bai san irin macen da za ta shigo gidansa ba. Yadda zamani ya canja, wadansu suna da mugun tanadi ga uwargida da ’ya’yanta. Idan da zaman fahimta za a yi, zama na shari’ar Musulunci, ai babu macen da za ta ki kishiya.”
A daidai lokacin nan sai ta yi firgigi ta mike zaune a kan gadon da take kishingide. Ba ta ankara da lokacin da mijinta ya shigo dakin ba, domin kuwa ga alama ya samu lokaci yana tsaye kusa da ita, amma wannan tunane-tunane da zancen zucci da take ta yi ne ya hana ta ankara.
“FATA, me ke faruwa ne? Kafin in shigo dakin nan, sai da na yi sallama har sau uku amma ba ki amsa ba. Hankalina ya tashi, na turo kofa na shigo. Na yi zaton ma ko wani rashin lafiya ne ya kama ki haka,” inji Alhaji Baba.
Ba ta amsa masa da kanzil ba, ta dai kura masa ido, kirjinta ya ci gaba da bugawa bal-bal-bal. Kai da ganin idanuwanta, ka samu tabbacin tana cikin kaduwa, fuskarta ta yi yaushi.
“Daddy! Wace ce Saratu Albishir?” Tambayar da ta yi masa ke nan, bakinta na rawa, idanuwanta na neman fitar da kwalla.
“Saratu? Wace ce kuma Saratu?” Inji shi.
“Ba mu haka da kai. Kada ka ce za ka boye mini wani al’amari komai muninsa. Kada ka mance da yanayin da muke zaune, cikin aminci da amanar juna.” Hankalinta ya kara tashi, duk da cewa ta samu natsuwar da ta rika zakulo masa tambayoyi masu cike da kalubale.
“Ni dai har yanzu ban ga dalilin wadannan tambayoyin ba…” Zai ci gaba da magana, amma sai Farida ta katse shi da wani kalubalen.
“Ta yaya za ka ce ba ka san dalilin tambayoyin nan ba. Ta yaya za ka mance abin da ya faru dazu? Shin wace ce ta shagaltu da kiran wayarka dazu, lokacin da muke kokarin ceto ’yarmu daga illar wutar lantarki? Ka mance yadda aka yi ta kiran wayarka, kai kuma kana ta faman kashewa? Ka mance yadda na ga sunan mai kiran naka, a lokacin da na miko maka wayar lokacin da ta kira ka?”
Ta samu kanta tana daga murya, a lokacin da take jero masa wadannan mabambantan tambayoyi. Ba halinta ba ne haka, domin kuwa ba ta yi masa musu a lokacin da suke tattaunawa. Ba ta daga masa murya koda tana cikin bacin rai da shi. Amma abin mamaki, ba ta san lokacin da haka ta faru da ita ba a yanzu.
“To, amma koma dai mene ne, yanzu a cikin daren nan za ki shiga yin hayagaga? Ba ki tunanin yara za su iya tashi daga barci?”
“Sun dade ba su tashi ba. Ba tashin barci ba, ni ko duniyar ma ai ban ki ta tashi ba!” Ta zumbura baki.
“Haba dai FATA! Wa ya gaya miki lokacin tashin duniya ya zo?” Ya kyalkyace da dariya, ya zauna kusa da ita. Ita kuwa sai ta yi tsagal ta mike tsaye, ta koma kuryar daki, kusa da kyaure, ta tsaya kikam.
“Lallai akwai bukatar duk abin da kake ciki ka shaida mini. Ni dai ban taba sanin wata mace mai suna Saratu ba, ko cikin danginka ko kuma cikin abokan huldarka ta kasuwanci. Bayan haka, lokacin da ta zabi ta kira ka, shi ma lokaci ne da ban taba ganin an matsa maka da kiran waya ba. Balle kuma ga shi mace ce ta nace da kiran.” Ta dan sarara da magana, shi kuwa ya ma rasa abin da zai shaida mata.
“Shin wace ce Saratu Albishir? Mece ce dangantakarka da ita?”
Za mu ci gaba