An karkare kada kuri’a
Sai fafutikar samun sa’a
An kawo karshen yi wa juna ba’a
An ji batuna ta cikin samma’a
Aikata miyagun laifuka mun ce a’a
Zugar zuganyewar zababaka
Ta haifar da baraka
Da rudanin shirya taruka
’Yan maula na kwaraka
Ba sa son daina wararar tufka
*
Jidali
Jerin jaddawali
Jalli-joga
Jajjagen jaga-jaga
Juyayin juyin juya-hali
*
Masu harkalla
Suna ta zilla
Da kulla gilla
Don su sa wasu kwalla
Har ai ta lalala
*
An fasko masu badala
Da ke tsalle-tsallen tsula
Da kulla-kulla
Ga yawan kutunguila
Wata ran sai an tsala musu bulala
*
Kowa ya daura damara
Al’umma na bukatar kira
Hankula duk su tattara
Mu lalubo hanyar warwara
Mar mu tsira daga asara
*
Mai-duka Yai mana sutura
Mui ta kai wa juna ziyara
Zumun zumunta a hallara
Mui wa juna kara
Kar a debi dukiyarmu ai kakara
*
Ina ’yan siyasa
Ban da kulla dasisa
Ban da sa-in-sa
A bari mu ci masa
Kafin ruwan damu ya tafasa
*
Mu kyautata dangantaka
Rani, damina da kaka
A shawo kan turka-turka
Mu daina shakka
Da talaka ake harka
*
Janjamin jan-ragama
Janye jaye-jayen jan-rigima
Tuni aikin gama
An ce ya gama
Sai mu nemi makama
*
Gusun da birnin Shehu
Al’umma na ihu
Sun gaza dora tukunya a murhu
An hana dura hatsi a buhu
Balle daure goriyar huhu
*
A birnin Dikko
Manyan dawa na kwankwadar koko
’Yan fashi na nan a loko
Sun yi dako
Jama’a an yi cirko-cirko
*
Jihar Zaman-fara
Ana ta kara
Masu garkuwa ba sa jira
Su ne a bakin masu hira
Dole ta sa a kai hattara
*
Masu mulki
Kui tsayin daki
A dauki kulki
Ai aikin kirki
Miyagu a taka musu birki
*
A birnin Dabo
An ce ba a dabo
’Yan boko na ta kwambo
Da bobo
Kashe fatari ne kwabo-da-kwabo
*
A lalubo bakin zare
A daina kai wa juna hare-hare
Munanan maganganu da harare-harare
Kishin al’umma ba kwanare
Sai an hada karfi a tare
*
A yasar da bambance-bambance
A daina ka ce-na-ce
Ko zaman zaure ai ta zance
Managartan manufofi kar mu mance
A aiwatar da ayyukan kulla kawance
*
A hana kwasar gararuma
Mui aiki girma-girma
A farmaki masu dama-dama
Komai a yi da kima
Ko a ce da dama
*
Mui wa kawunanmu masalaha
Mu sai komai da arha
Kar a buge da neman ahaha
A ci a sha
A ji dadin raha
*
Kasa ta washe, domin zababbakar zabukan shekarar dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa ta gangaro karshe, duk da cewa ana ta yawan hasashe-hasashe, amma abin da dai kawai ya rage shi ne furta batutuwa daga harshe, cewa ashe-ashe wadansu sun yi nashe-nashe da JIDALIN JADDAWALIN JALLI-JOGA. Koma dai mene ne aka tsuwurwurta a wajen zaben rukunin shugabannin al’umma a fadin Haurobiya, sai a tuna komai na da NAKASU, illa dai kawai ana son kwatanta abin da za a ce SAMBARKA, in ma son samu ne a samu NAGARGARU, amma ba fandararru masu fasa mana garu ba.
Baban-burin-huriyya da gama-garin gwamna gwarangwam lallai ku yi bitar batutuwan darussan makon nan, ta yadda za ku yi wa daukacin al’ummar kasar abin da ya dace wajen kawar wa kowa-da-kowa DUMUINIYAR DUGUNZUMAR DARKAKIN DAMUWA.
Babban batun da ke gaban Haurobiyawa dai, shi ne, bayan duk mun karkare sambatu da surutu rututu kan sakamakon alkaluman JIDALIN JADDAWALIN JALLI-JOGA, ai sai mu umarci zababbu su daina yawan babatu ko kulla kutu-kutu, su zo su dukufa ka’in da na’in wajen tunkarar dimbin matsalolin da suka yi wa al’umma kawanya a kowane bagire na rayuwa. A shawo kan GARKUWAR GAGARA KUWWA; GARARAMBAR GARA GARKEN GARAKA, uwa-uba zaman kashe fatari a tsakankanin masu fuka-fukin tashi, ta yadda za a rage musu radadin fushi kada su zo suna bushi ko rike harsashi da balati mai washi, har su sa wasu su kwashi kashi, karshe a karke da lallashi turka-turkar takun saka kuwa su ce babu fashi. Zababbun wakilai ban da rafkanuwar rafke al’umma.
’Yan makaranta ban da SUKA-DA-BURTSATSEN MAGANGANU game da sakamakon zabi-sonka a fadin Haurobiya, domin idan aka ga mummunar ta’asa a ko’ina aka tafka ta, to da hannun gama-garin al’umma da suka yi GWANGWAJEWAR GWANJON GANYEN GAYE da DAMBARWAR DANTSATSAR DAMATSA. Bisa wadannan dalilai ni ina ganin ya kamata a yaba wa Hukumar Zabi-sonka ta kasa, domin ta yi rawar gani ko da kuwa wani zai ce ai TAKA NA-ZUMBUDE ce.
Hakika akwai miyagun da suka yi DANNIYA DA MURDIYYA, HANDAMA DA BABAKERE. A duk inda suka samu sa’a akwai hadin gwiwar masu JAGWALGWALON JAGALIYA da SARA-SUKA; a duk inda irin wannan mummunar manufa ta ci kasa ko hakarsu ba ta kai ga ruwa ba, tabbas akwai al’umma masu kishi da ke da zakuwar ganin an kyauta yanayin zamantakewar Haurobiyawa, don gudun kada a karke da ZAMAN-TATTAKEWA. Lallai mu yi hattara, hankulanmu su tattara.
Batu na ingarman karfen karafuna tarragon kwangirin layin dogo, ba tare da laulayin wulwulawar hannayen agogo ba, sai da al’umma ta bayar da kafa aka samu sakamako a doron JIDALIN JADDAWALIN JALLI-JOGA. Wannan ne dalilin da ya sanya a kowane lokaci aka gudanar da zabi-sonka sai ka ji wadansu sun rankaya kotu don yin korafi, ko ma a yi ta tafka shari’a ta ki karkarewa. Haurobiyawa mu sauya, mu ga sauyi managarci, ta yadda kowa zai daina nukuburci don kasa ta fita daga kunci.