✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi za a yi gumurzu tsakanin Arsenal da Man City

A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila a jibi Lahadi ake sa ran za a yi gumurzu tsakanin kulob din Arsenal da na…

A ci gaba da fafatawa a gasar Firimiya ta Ingila a jibi Lahadi ake sa ran za a yi gumurzu tsakanin kulob din Arsenal da na Man City a wasa karo na 17.

Jadawalin gasar ya nuna, wasan zai gudana ne a filin wasa na Arsenal wato Emirates Stadium da misalin karfe biyar da rabi na yamma agogon Najeriya.

Sai dai kafin wasan, kulob din Manchester United zai hadu  da na Eberton da misalin karfe uku na rana agogon Najeriya.

Kawo yanzu kulob din Liberpool ne yake saman teburin gasar da maki 46 sai Leicester City ke biye da maki 38 sai Manchester City da maki 32 sai kulob din Chelsea mai maki 29.

Kulob din Arsenal yana matsayi na 9 ne da maki 22 da hakan ya sa ake ganin wasan na jibi zai yi zafi.

Arsenal ta yi wasa 9 a jere ba tare da ta samu nasara ba. Tarihi ya nuna rabon da kulob din ya shiga irin wannan hali tun a 1977 shekara 42 da suka wuce.

Idan za a tuna a makon jiya ne kulob din Manchesterr United ya lallasa na Manchester City da ci 2-1.