✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jibi za a fara gasar firimiya ta Najeriya

Kwamitin da ke da alhakin shirya gasar rukuni-rukunin firimiya na Najeriya (League Management Committee) ya bayar da sanarwar a jibi Lahadi 21 ga watan nan…

Kwamitin da ke da alhakin shirya gasar rukuni-rukunin firimiya na Najeriya (League Management Committee) ya bayar da sanarwar a jibi Lahadi 21 ga watan nan ne ake sa ran za a fara gasar wacce kungiyoyin kwallon kafa 20 za su fafata.
Kwamitin ya ce sun cimma wannan matsaya ce bayan sun tattauna da masu ruwa da tsaki a gasar da suka hada da shugabannin kungiyoyin kwallon kafar da ke fafatawa a gasar.
“A ranar 21 ga watan ne ne ake sa ran za a fara gudanar da gasar firimiya ta Najeriya”, kamar yadda sanarwar da kwamitin ya fitar a ranar Talatar da ta wuce.
Sai dai wadansu rahotanni da suka biyo baya sun nuna akwai yiwuwar a kara mako daya kafin a fara gasar ganin  yadda wadansu kungiyoyin kwallon kafa suka nuna ba su gama yin shiri ba.  Wasu kungiyoyin sun nuna har yanzu gwamnatocin jihohinsu ba su samar musu da kudin ka’ida na Naira miliyan 25 da kwamitin ya kayyade wa kowane kulob kafin ya fafata a gasar ba.  Hakan ta sa kwamitin ya fara yunkurin daga musu kafa zuwa makon gobe don ganin sun shirya tsaf kafin a fara gasar.
Kawo yanzu kungiyoyi da yawa da za su fafata a gasar sun biya kudin ka’ida na Naira miliyan 25 ciki har da kulob din Neja Tornadoes da ke Minna.
Idan za a tuna kungiyar kwallon kafa ta Enyimba ce ta zama zakara a bara.  Sai kungiyar Warri Wolbes ta biyu sai N asarawa United ta uku yayin da Wikki Tourist ta gama a matsayin ta hudu.
Kano Pillars wacce ta lashe gasarhar sau uku a jere ta kasance ta takwas a bara bayan ta hada maki 55.