✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jerin sunayen sabbin shugabannin PDP na kasa

Mutum 21 da za su ja ragamar jam'iyyar PDP.

Jam’iyyar PDP ta zabi sabbin shugabannin da za su jagoranci Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC).

An fitar da sabbin shugabannin su 21 ne a zaben da aka gudanar a babban baron jam’iyyar na Kasa da ya gudana da dandalin Eagle Square da ke Abuja a ranar Asabar.

18 daga cikin kujerun an tsaya takararsu ne ba tare da hamayya ba, in banda kujerun mataimakan shugaban jam’iyya da na shugaban matasa.

Ga jerin sunayen sabbin shugabannin:

 1. Dokta Iyorchia Ayu, Binuwai – Shugaban Jam’iyyar na Kasa
 2. Ambasada Ali Umar Iliya Damagum, Yobe – Mataimakin Shugaban Jam’iyya na yankin Arewa
 3. Ambasada Taofeek Arapaja, – Mataimakin Shugaban Jam’iyya daga yankin Kudu
 4. Muhammed Kadade Suleiman, Kaduna – Shugaban Matasa
 5. Sanata Samuel Anyanwu, Imo – Sakatare
 6. Hon. Yayari Mohamme, Gombe – Ma’aji
 7. Hon. Umari Bature, Sakkwato – Sakataren Tsare-tsare
 8. Daniel Woyengikuro, Bayelsa – Sakataren Kudi
 9. Farfesa Stell Effa-Attoe, Kuros Riba – Shugabar Mata
 10. Kamaldeen Adeyemi Ajibade (SAN), Kwara – Mashawarci kan Shari’a
 11. Hon. Debo Ologunagba, Ondo – Sakatare Watsa Labarai
 12. Okechukwu Obiechina Daniel, Anambra – Mai Bincike Kudi
 13. Arch. Setoji Kosheodo, Legas – Mataimakin Sakataren Jam’iyya
 14. Ndubuisi Eneh David, Enugu – Maitaimakin Mai Binciken Kudi
 15. Alhaji Ibrahim Abdullahi, Kebbi – Mataimakin Sakataren Yada Labarai
 16. Sanata Ighoyota Amori, Delta – Mataimakin Sakatare Tsare-tsare
 17. Hon. Adamu D.U Kamale, Adamawa – Mataimakin Sakataren Kudi
 18. Hajara Yakubu Wanka, Bauchi – Mataimakiyar Shugabaar Mata
 19. Timothy Osadolor, Edo – Mataimakin Shugaban Matasa
 20. Barisata Okechukwu Osuoha, Abia – Mataimakin Mashawarci kan Shari’a
 21. Hon. Abdulrahman Mohammed, Abuja – Mai Binciken Kudi.
%d bloggers like this: