Jam’iyyar PDP ta zabi sabbin shugabannin da za su jagoranci Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC).
An fitar da sabbin shugabannin su 21 ne a zaben da aka gudanar a babban baron jam’iyyar na Kasa da ya gudana da dandalin Eagle Square da ke Abuja a ranar Asabar.
- APC ta kwana da shirin kwashe komatsanta a 2023 —PDP
- An kara wa’adin hade layin waya da lambar NIN zuwa karshen 2021
18 daga cikin kujerun an tsaya takararsu ne ba tare da hamayya ba, in banda kujerun mataimakan shugaban jam’iyya da na shugaban matasa.
Ga jerin sunayen sabbin shugabannin:
- Dokta Iyorchia Ayu, Binuwai – Shugaban Jam’iyyar na Kasa
- Ambasada Ali Umar Iliya Damagum, Yobe – Mataimakin Shugaban Jam’iyya na yankin Arewa
- Ambasada Taofeek Arapaja, – Mataimakin Shugaban Jam’iyya daga yankin Kudu
- Muhammed Kadade Suleiman, Kaduna – Shugaban Matasa
- Sanata Samuel Anyanwu, Imo – Sakatare
- Hon. Yayari Mohamme, Gombe – Ma’aji
- Hon. Umari Bature, Sakkwato – Sakataren Tsare-tsare
- Daniel Woyengikuro, Bayelsa – Sakataren Kudi
- Farfesa Stell Effa-Attoe, Kuros Riba – Shugabar Mata
- Kamaldeen Adeyemi Ajibade (SAN), Kwara – Mashawarci kan Shari’a
- Hon. Debo Ologunagba, Ondo – Sakatare Watsa Labarai
- Okechukwu Obiechina Daniel, Anambra – Mai Bincike Kudi
- Arch. Setoji Kosheodo, Legas – Mataimakin Sakataren Jam’iyya
- Ndubuisi Eneh David, Enugu – Maitaimakin Mai Binciken Kudi
- Alhaji Ibrahim Abdullahi, Kebbi – Mataimakin Sakataren Yada Labarai
- Sanata Ighoyota Amori, Delta – Mataimakin Sakatare Tsare-tsare
- Hon. Adamu D.U Kamale, Adamawa – Mataimakin Sakataren Kudi
- Hajara Yakubu Wanka, Bauchi – Mataimakiyar Shugabaar Mata
- Timothy Osadolor, Edo – Mataimakin Shugaban Matasa
- Barisata Okechukwu Osuoha, Abia – Mataimakin Mashawarci kan Shari’a
- Hon. Abdulrahman Mohammed, Abuja – Mai Binciken Kudi.