Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya fitar da jerin ma’aikatun da sabbin Ministoci 45 da ya nada za su yi aiki.
Sai dai sabanin yadda aka saba gani a bayan, Shugaban ya yi wa ma’aikatu da dama kwaskwarima, sannan ya raba wasu, wasu kuma aka canza musu fasali.
Kazalika, Aminiya ta lura cewa duk da cewa Jihar Kano ta rabauta da kujerun Ministoci guda biyu, dukkansu za su yi aiki ne a matsayin kaanan Ministoci.
Ga cikakken jerin ma’aikatun da kowanne Minista zai yi aiki:
Tahir Mamman – Ilimi
Yusuf Sununu – Karamin Ministan Ilimi
Mohammed Badaru – Tsaro
Bello Matawalle – Karamin Ministan Tsaro
Ahmed Dangiwa – Gidaje da Raya Birane
Abdullahi T. Gwarzo – Karamin Ministan Gidaje da Raya Birane
Simon Lalong – Kwadago da Ayyuka
Hannatu Musawa – Al’adu
Atiku Bagudu – Kasafi da Tsara Tattalin Arziki
Mariya Mahmud – Karamar Ministar Abuja
Bello Goronyo – Karamin Ministan Ruwa
Abubakar Kyari – Noma da samar da Abinci
Yusuf M. Tuggar – Harkokin Waje
Sa’idu A. Alkali – Harkokin Cikin Gida
Ali Pate – Lafiya
Ibrahim Geidam – Harkokin ‘Yan Sanda
Maigari Ahmadu – Karamin Ministan Karafa
Shu’aibu Abubakar Audu – Karamin Ministan Karafa
Mohammed Idris – Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a
Nyesom Wike – Abuja
Lateef Fagbemi – Shari’a/Babban Lauyan Gwamnati
Imaan Suleiman Ibrahim – Karamar Ministar ‘Yan Sanda
Zephaniah Jisalo – Ayyuka na Musamman
Joseph Utsev – Ruwa da Tsafta
Aliyu Sabi Abdullahi – Karamin Ministan Gona da Samar da Abinci
Bosun Tuani – Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani
Ishak Salaco – Karamin Ministan Muhalli
Wale Edun – Kudi da Tattalin Arziki
Bunmi Tunji – Sufurin Jiragen Ruwa
Adedayo Adelabu – Lantarki
Tunji Alausa – Karamin Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a
Dele Alake – Ma’adinai
Lola Ade-John- Yawon Bude Ido
Adegboyega Oyetola – Sufuri
Doris Anite – Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari
Uche Nnaji – Kimiyya da Fasaha
Nkiruka Onyejeocha – Karamar Ministar Kwadago da Samar da Ayyukan Yi.
Uju Kennedy – Ministar Mata
David Umahi – Ayyuka
Festus Keyamo – Sufurin Jiragen Sama
Abubakar Momoh – Matasa
Betta Edu – Walwala da Yaki da Talauci
Ekperikpe Ekpo – Karamin Ministan Iskar Gas
Heineken Lokpobiri – Karamin Ministan Man Fetur
John Enoh – Wasanni
Majiyoyi daga Fadar Shugaban Kasa dai sun ce ba a kai ga sanya ranar rantsar da sababbin Ministocin ba, amma kwanan nan ake sa ran fara yi musu bita.