✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin Kasashen Da Aka Haramta Bikin Ranar Masoya

Saboda dalilai na addini, wasu kasashe sun haramta Ranar Masoya ta Valentine

An dade ana daukar ranar 14 ga watan Fabrairu a matsayin Ranar Masoya, inda mutane a sassan duniya ke bikin ranar ta hanyar ba da furanni da sauran kyaututtuka ga  wadanda suke kauna albarkacin ranar.

Sai dai duk da haka, akwai wasu kasashe da aka haramta yin bukukuwan ranar, saboda wasu dalilai.

Ga jerin kasashen:

  1. Saudiyya
  2. Iran
  3. Pakistan
  4. Malaysia
  5. Uzbekistan
  6. Indonesia

1. Saudiyya

Bikin Ranar Masoya ya saba da tsarin  ya saba wa akidar kasar Saudiyya inda aka haramta nuna soyayya a bainar jama’a.

Duk da cewa akwai ma’aikata kiristoci ’yan kasashen waje da yawa a Saudiyya, amma kasar ta haramta  duk abubuwna da suka shafi Ranar Masoya, kamar sayar da jajayen furanni ko teddy bear, da sauransu.

2. Iran

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta haramta samarwa ko sayarwa ko tallata duk wata kyauta ta Ranar Masoya, saboda kasar na kallon hakan a matsayin yada al’adun turawa.

Kasar ta gabatar da kudurin mayar da ranar ta zaman Ranar Mehregan, wani dadadden bikin al’adar kasar tun kafin zuwan Musulunci.

Hakan zai zama karramawa ga Yazata Mehr, wanda ke ganin da ya yada abota da kauna a cikin al’ummar kasar.

3. Pakistan

Pakistan, wacce ita ce kasa ta biyu mafi yawan Musulmi a duniya.

A ranar 7 ga Fabrairu, 2018, Babbar Kotun Kasar ta haramta bukukuwan Ranar Masoya da yada labaransa, bayan koke da wani dan kasa ya gabatar.

Duk da haka, wasu a Pakistan, musamman daliban jami’a da masu kasuwancin furanni da ke samun ciniki a lokacin, suka yi bikin ranar.

4. Malaysia

A shekara ta 2005 hukumomin Malaysia mai yawa Musulumai suka hana gudanar da bukukuwan Ranar Valentine, wanda ake zargi da haifar da yaduwar alfasha da badala a mutunci a tsakanin matasa.

A duk shekara ana gudanar da gangamin adawa da Ranar Masoya a kasar, kuma masu yin bikin  ranar ana iya tsare su.

5. Uzbekistan

Kasar Uzbekistan ta shahara da kare dogon tarihi da al’adu, kuma Musulunci shi ne babban addini kasar.

A shekarar 2012 sashen kula da tarbiyya da kyawawan halaye da ke karkashin hukumar ilimin kasar haramta irin wadannan bukukuwa a makarantu da cibiyoyin ilimi.

A maimakon Ranar Masoya, jama’ar kasar suke suna tunawa da ranar haihuwar jarumin kasarsu Babur, Sarkin Mughal duk da cewa gwamnatin kasar ba ta haramta Ranar Masoya ba, amma dai ba ya armashi a kasar domin girmama Sarki Babur.

6. Indonesia

Babu wata doka a hukumance da ta haramta bikin ranar a Indonesia.

Sai dai a ’yan shekarun nan, an yi zanga-zangar nuna bacin rai da zargin ranar da karfafa jima’i kafin aure da shan barasa, wadanda shari’ar Musulunci ta haramta su.

A wasu sassan kasar, irin su Surabaya da Makassar, inda galibin mutane ke da addini, ana amfani da dabarun tsoratarwa don hana bikin.

Duk da haka, matasa a Jakarta, babban birnin kasar, na ci gaba da gudanar da bukukuwan a bainar jama’a.