✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Kama Matasa Kan Yi Wa ’Yar Shekara 13 Fyade A Gona

Sun yi wa ’yar shekara 13 fyade a gona a garin Bajoga da ke Jihar Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu matasa biyu da ake zargin su yi wa wata ’yar shekara 13 fyade a gona a garin Bajoga, Karamar hukumar Funakaye.

Kakakin rundunar, Mahid Mu’azu Abubakar, ne ya bayyana haka a lokacin da ya gabatar da matasan da wasu da ake zargi su 20 a a shalkwatar rundunar.

ASP Mahid ya kara da cewa matasan da ake zargin an kama su ne bayan rahoton da nahaifin yarinyar ya kai caji ofis, inda yake zargin sun yi wa ’yarsa fyade.

ya ce a ranar 8 ga watan Fabarairu ne mahafin ya kai rahoto ofishin ’yan sanda da ke garin Bajoga cewa a ranar 7 ga wata matasan suka tare ’yar tasa a gona suka mata barazana, sannan suka yi mata fyade.

A cewarsa, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma da zarar an kammala bincike za a tura su zuwa kotu.