✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun kama rikakkun ’yan bindiga sun kwato kudin fansa a Abuja

Har da mata a cikin rikakkun ’yan bindigan da aka kama

’Yan sanda sun cafke wasu rikakkun ’yan bindiga guda bakwai, cikinsu har da mata biyu, suka kwato kudin fansa a hannunsu a Abuja.

Runduanr ’Yan Sanda Naira ta kama su ne da kufin fansa Naira miliyan tara a hannunsu da kuma makamai da rigar sulke da guraye da layoyi da kuma miyagun kwayoyi.

Kakakin rundunar CP Benneth Igweh, ya ce kudin da aka kama na fansa ne da dangin wani da suka sace suka biya

Da yake gabatar da su a safiyar Laraba, ya bayyana cewa wadanda ake zargin sun fito ne daga jihohin Naje, Filato, Katsina, Kaduna, Borno da kuma Abuja.

A cewarsa, sun amsa zargin da ake musu, kuma suna da hannu a garkuwa da mutae da aka yi a Abuja.

“Ana ci gaba da bincike kafin a gurfanar da su a kotu,” in ji shi.