Jawabin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi a kan saukin farashin man fetur a Najeriya ya jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar kasar yayin da wasunsu suka bayyana ra’ayinsu da baka wasunsu kuma ta kafafen sada zumunta.
A jawabin da Shugaban Kasar ya yi na cikar Najeriya shekara 60 da samun yancin kai ya ce, babu dace ba a ce man fetur ya fi tsada a Kasar Saudiyya fiye da Najeriya.
- Shekara 60: Mene ne sabo a jawabin Shugaba Buhari?
- Bikin shekara 60: Mun fi daukaka a dunkule —Buhari
A bayanin wani Dokta Ahmadu Ibrahim, ya ce ba abun mamaki bane don man fetur ya fi tsada a Saudiya idan aka lura da irin kulawar da Gwamnati ta ke bai wa ’yan kasarta.
“Idan ka lura, a saudiyya ana kula da lafiya ’yan kasa kyauta, kuma albashin su na dauke musu nauyin duk ababen more rayuwa da suka hada wutar lantarki da ruwa da iskan gas da fetur kuma ko nawa aka kayyade farashin man fetur karamin ma’aikaci zai iya siya ba tare da matsi ba.
“A Najeriya ana biyan karamin ma’aikaci Naira dubu 30 ne kacal, wadda ba zai ishe shi ya ciyar da iyalinsa ba balle ya kula da sauran ababen more rayuwa.”
“Idan za a yi wannan kwatance to ya kamata Buhari ya kara mafi karancin albashi, a kuma bayar ilimi da lafiya kyauta.”
Dokta Lawan Cheri, cewa ya yi, idan aka kalli abun ta fuskar tattalin arziki, “sayar da man kasar da yadda sauran kasashen da ke da arzikin man fetur zai hana Najeriya samun ribar man da take hakowa.”
“Da a ce muna tace man a cikin kasarmu, wannan daban, amma a matsayin gwamnati na mai kyautata rayuwar al’ummar ta ba neman riba ba, muna fatan gwamnati za ta yi amfani da kudin tallafin da ta zare wajen kyautata rayuwar ’yan kasa.”
Ita kuwa Aisha Abubakar cewa ta yi, “Bala’in da ’yan Najeriya suke ciki ba kadan ne ba, bai kamata Buhari ya yi wannan maganar a lokacin nan ba.”
The Hair plug a shafinta na Twitter cewa ta yi, “mafi karancin albashi a Saudiya Riyal 3000 ne wanda dai dai ya ke da kusan fiye da naira 300,000 yallabai, babu ma’ana su sayar da Litar mai N168 muka a sayar mana da ita Naira 161 inda mafi karancin albashi ya ke N30,000, hakan ya yi ma’ana?”