✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jarumin fim din Hausa Malam Yusuf Barau ya rasu

Jigon a masana'atar fin ta Kadawood ya rasu bayan an jima ana damawa da shi.

Allah Ya yi daya daga cikin dattawan masana’antar fim din Hausa, Malam Yusuf Barau rasuwa a Kaduna.

Shugaban masana’antar fim din Kaduna, Nura MC Khan ne ya sanar da hakan, inda ya ce, “Innalillahi wa in a ilaihi raji’un. Allah Ya yi wa Malam Yusuf Barau, fitacen jarumi a masana’antar fim din Hausa, rasuwa yanzu a gidansa da ke Kaduna.

“Za a yi jana’izarsa a Zariya kamar yadda addinin ya tanada. Muna rokon Allah Ya sa da shi da mala’ikun rahma.

Allah Ya hada mu a aljanna; Mun yi babban rashin na daya daga cikin jiga-jigan Kadawood”.

Malam Yusuf yana cikin dattawan masana’antar da suke dade ana damawa da su.