’Yan sanda sun tsinto gawarwakin mata hudu da wata jaririrya mai wata bakwai da suka nitse a kogi sakamakon hadarin kwalekwale a Karamar Hukumar Guri ta Jihar Jigawa.
Kakakin Rundunar ’yan Sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu ne ya bayyana hakan a Dutse, babban birnin jihar a ranar Laraba.
- Chelsea ta sallami kocinta, Thomas Tuchel
- An tsare mai shiga tsakani a sako fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna
“Bayanan da muka samu sun nuna da karfe 4:30 na yamma ne matan dauke da jaririyar suka hau kwalekwalen daga Karamar Hukumar Nguru ta Jihar Yobe zuwa kauyen Adiyani da ke Karamar Hukumar Guri a Jihar Jigawa.
“Sai dai an yi rashin sa’a jirgin kwalekwale ya kife da su a gab da inda za su sauka, amma matukin kwalekwalen ya tsira, amma sauran duk sun nutse,”in ji Shisu.
Ya ci gaba da cewa, “Masunta sun yi kokarin ceto su, sai dai sun riga sun rasu a lokacin da aka gano su.”
Kakakin ya ce an kai gwarwakin asibitin sha ka tafi na Adiyani, n da likitoci suka tabbatar da sun mutu.
Matan da aka gano sun hada da Oneyaniwura Kasagama mai shekaru 50 da Lafiya Bulama da Badejaka Kasagama da Gimto Kasagama da kuma Mai Madu Bulama, sai kuma jaririyar.
Kakakin ya ce dukkanin matan dai sun fito ne daga kauyen Adiyani.