✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jaridun Sifen sun ragargaji kulob din Real Madrid

A shekaranjiya Laraba ne jaridun da ake buga su a Sifen suka ragargaji kulob din Real Madrid jim kadan bayan kulob din ya yi wasa…

A shekaranjiya Laraba ne jaridun da ake buga su a Sifen suka ragargaji kulob din Real Madrid jim kadan bayan kulob din ya yi wasa da na Schalke 04 a gasar zakarun kulob-kulob na Turau (Champions League) a ranar Talatar da ta wuce, bayan ya sha kashi da ci 4-3 kuma ya sha da kyar da ci 5-4 a wasanni biyun da suka yi.

Da farko dai kulob din Madrid ya bi na Schalke 04 da ke Jamus har gida ne kuma ya lallasa shi da ci 2-0 kimanin makonni uku da suka gabata, amma abin mamaki sai aka wayi gari kulob din Schalke 04 ya bi na Madrid har gida a ranar Talatar da ta wuce kuma ya yi masa kaca-kaca da ci 4-3.
Sai dai duk da haka kulob din na Madrid ya haye wasan kwata-fainal a gasar, yayin da aka yi waje da na Schalke 04 na Jamus.
Jaridar Marca ta buga hoton golan Madrid Iker Casillas da kuma na Gareth Bale a shafinta na farko, inda ta yi musu sharhi a kan ‘yan kwallon da suka fi bayar da kunya a wasan yayin da ita kuma jaridar AS ta yi nata sharhin ne a shafinta na farko inda ta ce “duk da manya sun haye matakin kwata-fainal amma an so a yi abin kunya”, ma’ana da kyar kulob din na Madrid ya sha a gasar ta Champions League.
Jaridun sun bayyana mamakin ganin yadda ’yan kwallon Madrid suke shan kashi a ciki da wajen Sifen a ’yan kwanakin nan duk da irin makudan kudin da kulob din ya kashe wajen cefano zaratan ’yan kwallo. Hasalima jaridun sun tabbatar babu kulob din da yake kashe kudi a wajen cefanen ’yan kwallo kamar na Madrid amma abin mamaki sai aka wayi gari ’yan kwallon suna buga kwallo kamar wadansu ba su da laka a jiki. Hakan ta sa kawo yanzu kulob din ya kasa samun nasara a wasanni uku da ya yi a jere.
Jim kadan da tashi wasa a tsakanin Madrid da Schalke 04 a ranar Talatar da ta wuce ne sai magoya bayan kulob din Madrid suka rika yi musu ihu da kuma tofin Allah-tsine al’amarin da ya sa hatta kocin kulob din Carlos Ancelotti ya ce bai ga laifin magoya bayan nasu ba, ganin yadda ’yan kwallonsa suka kasa tabuka abin-a-zo-agani a wasan.
A makon jiya ma sai da kulob din billareal na Sifen ya rike wuyan na Madrid da ci 1-1 a gasar rukunin La-Liga ta Sifen a yayin da kulob din Atletic Bilabao kuma ya doke na Madrid a ranar Asabar da ta wuce da ci 1-0 al’amarin da ya sa kulob din FC Barcelona na Sifen ya kwace ragamar gasar ta La-Liga.
Alamu sun nuna muddin kulob din Madrid yana so ya kai bantensa a kakar wasa ta bana sai ya zage damtse tun da akwai wasanni masu zafi a gabansa. A karshen makon gobe ne ake sa ran kulob din zai hadu da na FC Barcelona a gasar rukunin La-Liga ta Sifen.