Jamus ta naɗa Julian Nagelsmann a matsayin wanda zai jagoranci tawagar ƙwallon ƙafar ƙasar.
A yanzu Nagelsmann shi ne zai jagoranci tawagar ƙasar a Gasar Kofin nahiyar Turai da Jamus za ta karɓi baƙunci a baɗi.
Tsohon kocin na Bayern Munich, ya sanya hannu kan kwantiragi har zuwa watan Yulin 2024, don haka zai iya barin aikin bayan an kammala gasar.
Kociyan mai shekaru 36, ya gaji Hansi Flick, da aka kora bayan rashin samun sakamako mai kyau a wasannin da ya jagoranta, wanda ya ƙare da Japan ta doke Jamus da ci 4-1 a farkon wannan watan.
Nagelsmann ya kasance bai da aiki tun bayan da Bayern Munich ta sallame shi a watan Maris, bayan ya yi ƙasa da shekaru biyu yana jan ragamar ƙungiyar.
Wasansa na farko zai kasance wasan sada zumunta da Amurka a Connecticut cikin wata mai zuwa.