✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jamus ta kyale ma’aikatanta su fara baccin rana a ofis saboda tsananin zafi

Jamus ta kyale ma’aikatanta su fara baccin rana a ofis saboda tsananin zafi

Kasar Jamus na duba yiwuwar kyale ma’aikata su fara yin baccin rana a ofis saboda yadda zafi yake dada tsananta a kasashen Turai.

A ’yan kwanakin dai kusan ilahirin kasahen Kudancin Turai na fama da tsananin zafin rana, lamarin da yake kawo barazanar yawan samun rashin lafiya ga mutane.

Johannes Niessen, Shugaban kungiyar ma’akatan lafiya na kasar ya ce ya kamata Jamusawa su fara bin sahun sauran kasahen Kudancin Turai wajen daukar matakai.

“A tashi da safe da wuri, a yi aiki tun da sanyin safiya sannan a dan yi bacci da tsakiyar rana,” kamar yadda ya bayyana a cikin wata hirarsa da kafar yada labarai ta RND.

Ko a ranar Laraba sai da kasar Italiya ta saka kusan biranenta 23 a cikin shirin ko-ta-kwana saboda yadda zafin ya tsananta, inda yake kai wa kusan maki 45-46 a matakin Celsius.

Kazalika, Ministan Lafiya Karl Lauterbach, a ranar Talata ya ce, “ina ganin babu wata matsala idan aka ba ma’aikata damar dan rintsawa da rana lokacin aiki”, kodayake ya shawarci masu daukar aiki da ma’aikata su shawarta tsawon lokacin da za a rika baccin.