Wani kwararre a Cibiyar Binciken Tattalin Arziki ta Jamus (DIW), Guido Baldi, ya ce cibiyar na ganin cewar kasar ta fada halin matsin tattalin arziki.
Baldi ya fada a ranar Laraba cewar akwai yiwuwar yakin da ake gwabzawa tsakanin Ukraine da Rasha ya yi sanadiyyar koma-bayan tattalin arzikin kasar da kashi biyar a shekarun 2022 da 2023.
- Kotu ta hana magoya bayan Peter Obi yin gangami a Legas
- Za a fara kama masu karnukan da ba su yi musu rigakafi ba a Anambra
Ya kara da cewa, tashin farashin makamashin da ake fama da shi zai haifar da asara a fannin lantarki wanda hakan babbar barazana ce ga kamfanoni da dama a kasar.
Masanin ya kuma ce hauhawar farashin makamashi da kuma rashin tabbas na ci gaba da yi wa harkokin kasuwanci tarnaki a kasar.
“Nan ba da jimawa ba tambayar da za ta kunno kai ita ce, ko kamfanoni a kasar za su iya ci gaba da gudanar da harkokinsu da wannan yanayi da ake fuskanta,” inji Laura Pagenhardt wanda shi ma kwararre ne a cibiyar ta DIW.