✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jam’iyyu 11 sun nesanta kansu da boren PDP a wurin karbar sakamakon zabe

Jam'iyyu 11 daga cikin 18 da ke Najeriya sun nesanta kansu da matakin babbar jam'iyyar adawa ta PDP

Jam’iyyu 11 daga cikin 18 da ke Najeriya sun nesanta kansu da matakin babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi na kaurace wa cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa da ke gudana a Abuja.

Ana cikin tattara sakamakon zaben ranar Litinin a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Abuja ne wakilin PDP, Sanata Dino Melaye, ya rika tayar da jijiyar wuya cewa dole sai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tabbatar da cewa duk sakamakon zaben shugaban kasa da za a gabatar a wurin, kafin a sanar da shi sai an sanya shi a shafin tattara sakamakon zabe mai iRev, tun daga matakin rumfar zabe.

Dino Melaye da takwaransa kuma tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Emeka Ihedioha, sun daga cewa wajibi ne a sanya sakamakon zaben a shafin iRev inda kowa zai iya budewa ya gani domin tabbatar da yin komai a fili.

A kan haka ne Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ke jagorantar tattara sakamakon zaben, ya bayyana cewa babu wani sakamakon zaben da kawo gabansa, face sai jami’an zabe da wakilan jam’iyya sun amince sun kuma sanya hannu a kai tun daga rumfar zabe.

Idan an kammala sai a kai zuwa ofishin tattara sakamakon zabe na gunduma, inda a nan ma, a kan idon wakilan jam’iyyu za a tantance tare da tabbatar da sahihancinsa.

Daga nan wuce zuwa matakin karamar hukuma a yi makamancin haka, kafin a je matakin jiha, shi ma a yi haka, sannan daga karshe a kawo zuwa matakin kasa..

Duk da haka, Melaye ya ci gaba da hayagaga, cewa ba za ci gaba da aikin ba, sai hakarsu ta cimma ruwa, lamarin da ya sa Yakubu ya gargade su da kada su kawo hatsaniya ga aikin tattara sakamakon zaben.

Amma da ba su gamsu ba, sai Melaye ya fice, wanda ficewarsa tare da Ihedioha ke da wuya, wasu suka bi shi.

Duk da haka, aka ci gaba da tattara sakamakon zaben, inda ana cikin haka wasu jam’iyyu suka fito suka nesanta kansu da abin da wakilin PDP da magoya bayansa suka yi.