✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Jam’iyyar APC ta kara wa’adin rajistar mambobinta

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta kara wa'adin rajistar mambobinta da mako uku

Jam’iyyar APC mai mulki ta tsawaita wa’adin yin rajistar mambobinta da mako uku.

Sanarwa da Sakataren Kwamitin rikon APC na kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fitar ranar Alhamis ta ce karin wa’adin ya zama dole saboda yawan mutanen da ke son shiga jam’iyyar.

“Yawancin jihohi, saboda dalilai daban-daban, na bukatar karin lokaci don kammala aikin.

“Yawaitar mutane da manyan masu ruwa da tsaki ya sa akwai bukatar tsawaita lokaci don ’yan Najeriya masu muradin shiga cikin jam’iyyar samu dama.

“Kwamitin riko da Shirye-shiryen Taron (CECPC) a karkashin jagorancin Mai girma, Mai Mala Buni ya yi duk mai yiwuwa don kiyaye wa’adin da ya gabata, amma ya zama wajibi a tsawaita lokacin wannan muhimmin aiki.

“Sakamakon haka, CECPC ta amince da shawarar tsawaita wa’adin aikin na tsawon makonni uku,” inji shi.