Tanko Nuru jami’in da ya lura da yadda wasa ya kaya a tsakanin Kano Pillars da Ikorodu United (Match Commissioner) ya rasu. An tsinci gawarsa ce a Otel din da ya sauka a Kano.
dan asalin Jihar Nasarawa, an ce ba a san dalilin rasuwar tasa ba. Jim kadan bayan an kammala kwallo a tsakanin Pillars da Ikorodu United wanda ya kasance jami’in da ya lura da yadda wasan ya kaya ne (Match Comissioner) sai ya nufi masaukinsa a wani Otel da ba a ambata ba, inda a washegari ne aka tsinci gawarsa. Labarin rasuwar tasa ya bazu ne bayan kulob din Ikorodu United ya watsa a shafin sadarwarsa na Twitter.
Kulob din Pillars da na Ikorodu United sun fafata ne a gasar firimiya ta kasa.
Jami’in da ya lura da wasan Kano Pillars da Ikorodu United ya mutu a Otel
Tanko Nuru jami’in da ya lura da yadda wasa ya kaya a tsakanin Kano Pillars da Ikorodu United (Match Commissioner) ya rasu. An tsinci gawarsa…