Shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe Farfesa Umar Pate, ya ce jami’ar za ta zama cibiya ta biyu a Najeriya baya ga Jami’ar Ilorin a bangaren bincike da nazari kan suga.
Farfesa Pate, ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabanin jami’ar suka kai wa Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya wata ziyara a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gombe.
- Rashin tsaro: Majalisa ta bukaci a dage kidayar 2021
- Yadda aka raba wa marayu 1,100 kayan sallah a Kano
Ya ce Jami’ar Tarayya ta Kashere (FUK) tamkar sauran jami’o’i a kasar nan ce da suka yi fice kuma ake daraja shaidar karatunsu ko’ina a fadin duniya.
Pate, ya ce don ganin jami’ar ta kasance cibiyar bincike kan suga, ya sanya suke rokon gwamnati da ta basu Cibiyar Koyar da Aikin Gona ta Leventis da ke garin Tumu da zummar hade ta da jami’ar wanda kamfanoni irin su BUA da Dangote za su dinga ziyartarsu don yin nazari.
Ya kuma nemi gwamnati ta samar musu da karin fili domin fadada gine-ginen jami’ar da suka hada da azuzuwan karatu da dakunan kwanan dalibai.
A cewarsa, yanzu suna son jami’ar ta zama ta yi fice a bangaren fasahar sadarwar zamani wacce za a yi tunkaho da ita a ko’ina.
A nasa bangaren, Gwamna Yahaya ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da taimakawa jami’ar kamar yadda ta saba, inda ya ce zai tuntubi Kwamishinan Kasa da Safiyo na jihar don ganin yadda za a bullowa batun karin filin jami’ar wajen biyan diyya ga wadanda suka mallaki filaye a kusa da ita.
Gwamnan ya ce batun hade Cibiyar Koyar da Aikin Gona ta Leventis da ke garin Tumu da jami’ar kuwa suna da kyakkyawar fahimta da su wanda idan an tashi hakan ba zai zama da matsala ba.