Yayin da take shirye-shiryen sake manyan makarantu ranar 18 ga watan Janairun 2021, Jami’ar Bayero dake Kano ta umarci ma’aikatanta wadanda ayyukansu ba su zama wajibi ba da su zauna a gida.
Wadanda lamarin ya shafa dai sune ma’aikatan dake matakin tsarin albashi na CONTIS11/CONUASS 04 zuwa kasa.
- Jami’ar Bayero Kano ta ce za a kammala zangon karatun 2019/2020
- Saudiyya ta wajabta wa alhazai yin allurar rigakafin COVID-19
Sakataren Sashen Watsa Labarai na Jami’ar, Lamara Garba shine ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, wadda ya ce hakan umarni ne daga Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC).
Sai dai ya ce za su dawo domin ci gaba da ayyukansu kamar yadda aka saba a ranar da aka ayyana a shirye-shiryen sake bude jami’ar.
Sanarwar ta ce, “Har ya zuwa lokacin da za a dawo aiki ka’in da na’in, kada wani ma’aikaci ya kuskura ya yi kowacce irin tafiya ba tare da izini ba.
“Ma’aikata su lura cewa za a iya kiran kowannensu domin yin aiki idan bukatar hakan ta taso.
“Ma’aikatan da za su zo aiki ko masu zuwa ziyara cikin jami’ar mu dole ne su kiyaye ka’idojin matakan kariyar COVID-19,” inji sanarwar.
BUK ta kuma shawarci wadanda suka yi tafiya a kwanan nan zuwa kasashen ketare das u killace kansu sannan su tuntubi sashen yaki da cutar ta COVID-19 na makarantar domin taimakon gaggawa.