Gwamnatin Jihar Kano ta mayar da martani kan ƙorafe-ƙorafen da masu gine-gine a kan titin BUK suka yi, bayan da Ma’aikatar Ƙasa da Tsare-tsaren Birni ta sanya musu jan fenti.
Masu gine-ginen sun koka kan cewa alamar na nufin gwamnati na shirin rushe ko ƙwace musu kadarorinsu.
- Sojoji Sun Kashe ’Yan Boko Haram 9 Sun Kwato Makamai
- Dan sanda ya harbe mahaifinsa har lahira a Borno
An sanya wa gine-ginen alama ne a ranar 10 ga watan Yuli, 2024, yayin da a baya gwamnatin jihar ta rushe wasu daga cikinsu.
Gwamnatin ta bar wasu daga cikin gine-ginen ne bayan ƙorafe-ƙorafe da kiranye-kiranye da wasu al’ummar jihar suka yi a baya.
Alamar da aka sanya a kwanan nan ta bai wa masu gine-ginen mamaki, inda suke roƙon gwamnati ta sake duba lamarin.
Ibrahim Mu’azzam, ɗaya daga cikin masu kadara a yankin, ya ce, “Mun tashi muka ga jan fenti a gidajenmu, kamar bara lokacin da KNUPDA ta yi haka. Mun yi ƙoƙari mu hana amma muka ƙare a kotu, yanzu kuma hakan na sake faruwa.
“Mun sa yi waɗannan wurare ne a lokacin gwamnatin baya. Yawancin masu gidajen yanzu sun siya ne a hannun wasu. Lokacin da muka sayi wajen, ana yawan aikata laifuka. Amma samar da gine-gine ya taimaka wajen rage laifuka.
“Mun saka kuɗi sosai wajen inganta wajen nan, wanda a baya tafki ne. Mun yi ƙoƙarin sosai wajen gina wajen nan. Gwamnati ba ta sanar da mu komai game da alamar ba. Muna buƙatar gaskiya da adalci. Mu ‘yan Kano ne kuma mu ne muka zaɓi wannan gwamnati. Wannan shi ne abin da ya dace a yi mana? Muna roƙon Gwamna ya yi mana adalci, kamar yadda muka goyi bayansa lokacin gwagwarmayar shari’arsa. Mu ‘yan kasuwa ne da ke ƙoƙarin taimaka wa ci gaban jiharmu da tattalin arziƙinta.”
Masu gine-ginen sun yi kira ga gwamnati ta guji ɓata kuɗi kan abin da ya shafi shari’a.
A martaninsa, Abduljabbar Umar, Kwamishinan Ƙasa da Tsare-tsaren Birni, ya ce gwamnati na binciken kan yadda suka mallaki gidajen kuma za a fitar da sakamakon nan ba da jimawa ba.
Ya bayyana, “Wajen yana kan hanyar ruwa tare da tafkuna da tsohuwar ganuwa mai muhimmanci. Mun sanya alamar ne saboda akwai matsala. Dole ne mu kare tare da tsara birni yadda ya kamata. Mun samu ƙorafe-ƙorafe kan waɗannan gidaje kuma mun bincika da kanmu.
“An gina wasu gidaje ba daidai ba, wanda ya haifar da matsalolin ambaliyar ruwa. Dukkaninmu na da hakkin kare muhalli. Mun yi namu aikin bincike kuma nan ba da jimawa ba za mu ɗauki mataki. Gwamnati tana yi wa jama’a aiki kuma ba za ta cutar da su ba tare da dalili ba.”