✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama lakcarorin bogi a Jami’ar BUK

Lakcarorin bogin sun bayyana wa daliban cewa sayen litattafansu wajibi ne kuma babu wanda zai ci jarabawa sai wanda ya saya

Wasu malaman jami’a na bogi sun shiga hannun jami’an tsaro a Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Dubun nalaman jami’an bogin ta cika ne a yayin da suke tsaka da sayar wa dalibai ’yan ajin farko da litattafan karatu.

Sanarwar da jami’ar ta fitar ɗauke da sa hannun Mukaddashin Magatakarda Jami’ar BUK Bala G. Abdullahi, ta ce lakcarorin bogin  sun tursasa dalibai sayen litattafansu guda hudu a matsayin sharadin cin jarabawar darussan su.

Ya ce dubun mutanen biyu, Mista David Iluebe daga Jigar Edo da Mista Chike E. Eke daga Jihar Delta, ta cika ne bayan sun shiga dakin karatu a Tsangayar Karatun Injiniya, suka gabatar da kansu a matsayin lakcarori, suka tallata musu litattafai hudu.

Lakcarorin ba su tsaya nan ba, sun bayyana wa daliban cewa sayen litattafan wajibi ne kuma babu wanda zai ci jarabawa sai wanda ya saya.

Magatakardan ya ce barazanar ta tilasta wa daliban sayen litattafan, amma daga bisani take-taken lakcarorin bogin ta sa jami’an tsaron jami’an kama su.

Bayan samun korafi aka kama su, inda a halin yanzu ake tuhumar su da laifukan kutse, sojan gona, damfara da kuma cuta.

Ya ce lakcarorin bogin sun bayyana cewa karo ba biyu ke nan da suka yi haka a Kano, domin a baya sun yi a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta jihar (Kano Poly).

Sun yi ikirarin wallafa littatafan da suke sayarwa kuma sun yi haka ne saboda rashin aiki.