Hukumar Gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da dakatar da ɗaukar darusa zuwa wani lokaci, sakamakon zanga-zangar adawa da yunwa da ake ci gaba da yi a faɗin Najeriya.
Wata sanarwa da Jami’ar ta fitar ranar Litinin, ta ce ta ɗauki matakin ne bayan zama da ta yi da duba batun zanga-zangar da ake yi.
- Rasha ta nesanta kanta da zanga-zangar Najeriya
- Zanga-zanga: Tinubu ya gana da shugabannin tsaro a Aso Rock
“Mun damu da lafiyar ɗalibai da kuma dukiyoyinsu, shi ya sa muka ɗauki matakin.
“Muna kira ga ɗalibai da ma’aikatanmu da su ci gaba da kula da irin zirga-zirgar da za su yi a wajen Jami’a domin kaucewa shiga hatsari.”
Jami’ar ta kuma shawarci ɗaliban da ke zaune a cikin makarantar da su kwantar da hankalinsu, sannan su kasance masu bin doka da oda.
Kazalika, Jami’ar ta bayar da tabbacin komawa ɗaukar darusa da zarar al’amura sun daidaita a jihar.