Jami’ar East Carolina ta kasar Amurka ta bayyana takaicinta bisa matsayin farfesa da wani ma’aikacinta ya ba Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, ba da izinin hukumar gudanarwarta ba.
A amsar jami’ar ga takardar da Gandujen ya aike mata na neman ta ba shi hakuri bisa nadin bogi da aka yi masa, jami’ar ta ce dukkan abun da takardar nadin ta kunsa ba da yawunta ba ne.
Yawan Mutanen Najeriya yanzu ya kai miliyan 206 – NPC
Takardar ban hakurin, Mataimakin Shugaban Jami’ar a fannin harkokin karatu, Dokta B. Grant Hayes, ya sa wa hannu, jami’ar ta ce ba da izininta aka yi nadin ba kuma ba ta da niyyar aibata gwamnan.
“Muna takaicin faruwar lamarin da ya haifar da torzarci, wanda aka yi ba da sanin Jami’ar Carolina ba, na aikewa da wasikar”, inji shi.
Ofishin Kwamishinan Yada Labai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya fitar da wasikar da jami’ar ta aike wa gwamnan.
Cece-kuce kan nada Ganduje Farfesa
A kwanakin baya, gwamnan ya aike da takardar neman jami’ar ta ba shi hakuri kan nadin Farfesan bogi da aka aiko masa cewa yi masa.
Bayan fitar labarin nadin gwamnan ne kwatsam daga bisani hukumar gudanarwar jami’ar ta East Carolina, ta fito ta musanta, tana mai cewa bada yawunta aka yi ba.
Da alama matakin da jami’ar ta dauka na ban hakurin zai kawo karshen takaddamar da aka shafe kusan mako guda ana ce-ce-ku-ce musanman a kafafen sa da zumunta.