Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi ta sallami ɗaya daga cikin malamanta, Dokta Usman Mohammed Aliyu daga jami’ar bisa zargin neman yin lalata da wata ɗaliba matar aure da ke karatun digiri na biyu.
Idan dai ba a manta ba, Kamila Rufa’i Aliyu, ɗalibar Sashen koyon aikin injiniya ce, a shekarar bara ta roƙi mahukuntan Jami’ar ta hannun tsangayarsu da su binciki lamarin.
- Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
- An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace
Ɗalibar ta kuma zargi Dakta Aliyu da yi mata barazanar rashin samun nasarar karatunta idan har ta ƙi amincewa da biyan buƙatarsa.
Malamin da ya samu labarin ƙarar da aka shigar da shi, an shigar da ƙarar a gaban kotu a kan zargin ɓata suna a kan wata ɗaliba, tsangayar da Jami’ar.
Amma Jami’ar a cikin Jaridarta (ATBU Herald) ta Afrilu 22, bugu na Vol. 39 lamba ta 5 ta bayyana cewa majalisar gudanarwa ta jami’ar ta kori Dakta Usman Mohammed Aliyu daga aiki a jami’ar.
Jaridar ta ce: “A zamanta na yau da kullun karo na 96 da aka gudanar a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu, 2025, Majalisar ta amince da korar Dakta Aliyu bisa laifin neman yin lalata da ɗalibar.”
Rahoton ya ce korar ta biyo bayan wani rahoton da kwamitin ladabtarwa na manyan ma’aikatan ya yi wanda ya same shi da aikata laifin.
“Sanarwar ta ci gaba da cewa korar ta biyo bayan babi na 3, sashi na 1, (o) na sharuɗɗan manyan ma’aikatan jami’ar.