✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara biyan dalibai kuɗin tallafin karatu

Nan da makonni biyu za a kammala biyan daliban wasu manyan makarantu 55

Daliban manyan makarantu a Najeriya sun fara karɓar kudin tallafin karatu na wata-wata daga Gwamnatin Tarayya.

Asusun Tallafin Karatu na Ƙasa (NELFUND) ya bayyana cewa tuni dalibai 20,371 da suka yi nasara daga manyan makarantu shida a fadin Najeriya suka samu kuɗin tallafinsu na watan Yuli.

Manajan-Daraktan NELFUND, Mista  Akintunde Sawyerr, ya ce nan da makonni biyu za a kammala biyan daliban wasu manyan makarantu 55.

Manyan makarantun da aka fara da biyan ɗalibansa su ne:

  1. Jami’ar Bayero ta Kano (BUK)
  2. Jami’ar Maiduguri, Jihar Borno
  3. Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, Katsina
  4. Jami’ar Ilorin, Jihar Kwara
  5. Jami’ar Benin, Jihar Edo
  6. Jami’ar Ibadan, Jihar Oyo

A cewarsa, nan da makonni biyu za a kammala biyan daliban wasu manyan makarantu 55.

Sawyerr ya ce NELFUND za ta yi duk abin da ya dace domin ganin daliban da ke cin gajiyar tallafin karatun suna samun kuɗaɗensu a kan lokaci.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce biyan kuɗin tallafin na nuna irin aniyar Shugaba Tinubu na ganin cewa ɗaliban Najeriya sun samu tallafin kuɗaɗen da suke buƙata domin samun ingantaccen ilimi.

Daraktan Kuɗi na NELFUND, Ibom Uche, wanda shi ne ya sanya hannu kan sanarwar, ya ce Tinubu ya ba da ƙarin Naira biliyan 50 domin dalibai su amfana.