✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Amurka: CSU ta tabbatar cewa Tinubu dalibinta ne

Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka ta tabbatar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu dalibinta ne da ya kammala digirin farko a 1979

Jami’ar Jihar Chicago (CSU) da ke Amurka ta tabbatar cewa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu tsohon dalibinta ne da ya kammala digirinsa na farko a shekarar 1979.

Jami’ar CSU ta bayyana haka ne ta wata takarda da ta aike wa CBS, wata fitacciyar kafar yada labarai a Amurka ranar Alhamis.

Sai dai ta bayyana cewa dokokin Amurka sun haramta mata bayar da karin bayanan karatun dalibi ba tare da izininsa ba, sai dai idan kotu ce ta umarce ta.

Babban abokin hamayyar Tinubu kuma dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2023, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yana zargin Tinubu da amfani da takardun  bogi na shaidar kammala karatun a Jami’ar CSU a 1979.

A kan haka ne yake neman kotun saurarron kararrakin zaben shugaban kasa ta soke nasarar Tinubu ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Aminiya ta ruwaito wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Durojaiye Ogunsanya, yana cewa ajinsu daya da Tinubu a CSU, kuma tare suka kammala.

Durojaiye ya shaida wa gidan talabijin na TVC cewa su biyun sun yi karatu ne a fannin Aikin Akanta da Gudanar da Mulki na jami’ar kuma a shekarar 1979 da suka kammala Tinubu ne shugaban  kungiyar daliban sashen.

Atiku dai ya shaida wa kotu cewa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na 2023 cewa gabatar wa hukumar zabe (INEC) takardun bogi domin tsayawa takara da Tinubu ya yi dalili ne na soke zabensa.

Kimanin mako biyu ke nan da ta yi watsi da bukatarsa ta soke zaben Tinubu bisa hujjar cewa, a baya lokacin da Tinubu yake Gwamnan Jihar Legas, kotu ta riga ta yanke hukunci a kan makamanciyar karar, inda ta yi watsi da shi.

Duk da haka Atiku bai hakura ba, inda a makon nan lauyoyinsa suka gabatar wa babbar kotun Amurka bukatar ta tilasta wa CSU fitar da bayanai da takardun shaidar karatun Tinubu.

Kawo yanzu dai, Mai Shari’a Jeffrey Gilbert na kotun da ke zama a yankin Illinois bai yanke hukuci kan bukatar ba tukuna.

Dalilin takaddamar

Wani abin da ake takaddama a kai game da sahihancin takardar shaidar karatun Tinubun shi ne wanda ya sa hannu a kanta.

Shugaban Jami’ar Elnora Daniel ne dai ya sanya hannu a kan takardar da Tinubun ya gabatar wa INEC, amma kuma Daniel bai fara aiki a CSU ba sai a 1998, bayan shekara 19 da yaye ’yan ajin su Tinubu.

A yayin zaman kotun a Amurka, lauyan CSU Michael Hayes, ya shaida wa Alkali Gilbert cewa jami’ar ba za ta iya tantance shaidar karatun Diplomar Tinubu ba.

Amma wani kakakin CSU ya tabbatar cewa Tinubu ya kammala jami’ar.

Ya bayyana cewa CSU ba za ta iya tantance takardar diplomar ba ne saboda takardar ba ta daga cikin takardun karatu, wani abu ne kawai na al’ada, amma ba ya cikin kundin takardun bayanan karatun dalibi.