Jami’ar Abuja ta kaddamar da aikin sintiri na sa’a 24 a cikin harabarta da kewaya ta hanyar amfani da mafarauta da ’yan banga domin dakile ayyukan ’yan bindiga.
Uban Jami’ar Abuja, Modibbo Mohammed, ya ce an dauki matakin ne bayan harin ’yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu ma’aikata a rukunin gidajensu da ke cikin jami’’ar.
- Halin da makarantun Tsangaya na gwamnati ke ciki a Kano da Jigawa
- Yadda ’yan IPOB suka sare kan abokin aikinmu suka kone gawarsa — Dan sanda
“Mun dauki mafarauta da ’yan banga su rika gudanar da sintiri a yankin da babu katanga saboda filin jami’ar na da girma sosai,” inji shi.
Uban Jami’ar Abuja ya shaida wa taron manyan shugabanni da jami’an gudanarwa da na kungiyoyin jami’ar cewa suna yin duk mai yiwuwa domin ganin ba a sake kai hari ba a jami’ar.
Da yake magana game da halin da gidajen ma’aikatan jami’ar suke ciki, ya ce, “Gidajen ma’aikatanmu ba su kai yadda ake bukata ba, har kunya nake ci game da irin gidajen da ma’aikatanmu suke zaune a ciki.”
Amma ya ce, “Kwamitin gudanarwar Jami’ar ya yi zama da Ministan Abuja a kan lamarin kuma ministan ya yi alkawarin daukar mataki a kai, nan ba da jimawa ba.
“Nan gaba kadan kuma za mu tura wakilanmu zuwa hukumar FERMA domin ta bayar da muhimmanci wajen gyara hanyoyin da ke cikin jami’ar,” inji shi.
Ya kara da cewa, “Tabbas za mu yi hadin giwa da hukumomin gwamnati tare da janyo kamfanoni masu zuba jari su tattauna da gwamnati kan yadda za a samar wa ma’aikatan wannan jami’a irin muhallin da ya dace da matsayinsu na malaman jami’a.”