✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

DSS ta rufe ofishin PDP saboda Gwamnan Ondo

Jami'an DSS da ’yan sanda sun rufe ofishin PDP na Ondo, inda jama'a ke neman gwamnatin jihar ta bayyana inda Gwamna Akeredolu ya shige

Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS da kuma ’yan sanda sun rufe sakatariyar jam’iyyar adawa ta PDP ta Jihar Ondo.

Hukumomin tsaron sun dauki matakin ne a safiyar Litinin a daidai lokacin da al’ummar jihar suke gunaguni da neman gwamnatin jihar ta bayyana musu inda Gwamna Rotimi Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki.

Ana zargin hukumomin tsaron sun rufe ofisihin jam’iyyar ne sakamakon shirin wasu ’yan jam’iyyar na gudanar da zanga-zanga kan rashin kasancewar gwamnan a jihar na tsawon lokaci.

Da farko Gwamna Akerodule wande ke fama da rashin lafiya da ba a bayyana ba, ya shafe wata uku a kasar Jamus, inda yake jinya, kafin ya dawo jihar a watan Satumba.

Tun bayan dawowar gwamnan, ya ci gaba da zama a gidansa, da ke birnin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, lamarin da ya sa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a jihar kiraye-kirayen ya sauka daga mukaminsa.

A ranar Lahadi PDP ta yi barazanar jagorantar wani gagarumin zanga-zanga a birnin Akure a yau Litinin, domin neman sanin inda Mista Akeredolu yake da kuma halin da yake ciki da ya hana shi zama a Jihar Ondo.

Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani kan halin da ake ciki daga kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Ondo Funmilayo Odunlami-Omisanya, amma hakar ba ta cim-ma ruwa ba.