Jami’an tsaro sun kashe ’yan tawaye 38 tare da kame wasu 78 a wani samame a yankin Badakhshan da ke Arewacin kasar Afganistan.
Shugaban Sashen Yada Labarai da Al’adu na Lardin Qari, Maazudin Ahmadi ne, ya bayyana haka a ranar Litinin.
- Batanci ga Annabi: Salman Rushdie ya zama mai ido daya
- DSS ta tabbatar da sanarwar shirin harin ’yan ta’adda a Abuja
Ahmadi ya shaida wa manema labarai cewa, “A yayin da ake gudanar da aikin tsaftace muhalli a yankunan Shiwa, Arghanj Khwa da Ragh cikin mako guda da ya gabata, an kashe ’yan tawaye 38 da ke dauke da makamai tare da cafke wasu 78.”
Jami’in ya kara da cewa an kashe jami’an tsaro uku tare da raunata wasu biyar a samamen.
A halin da ake ciki, kamfanin dillancin labarai na Bakhtar ya rawaito cewa, kwamandojin ’yan tawayen biyu, wato Bahrudin da Abdul Hamid, na daga cikin wadanda aka kashe a samamen na mako guda.