Rundunar tsaro ta musamman da ta kunshi sojoji da ’yan sanda da kuma ’yan Sa-kai a Jihar Neja ta ce ta murkushe wani da ’yan bindiga suka yi yunkurin kai wa a garin Bangi, hedkwatar Karamar Hukumar Mariga ta jihar.
Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 6:00 na safiyar Laraba, lokacin da gungun ’yan bindigar suka yi kokarin shiga garin.
- Majalisa na so a fara ba masu ‘first class’ aiki da zarar sun kammala digiri
- Buhari ya nemi gafarar ’yan Najeriya kan wahalar mai
Mazauna yankin sun ce jami’an tsaro sun kawo agajin gaggawa, inda aka samu nasarar kashe sama da 100 daga cikinsu.
Kwamishinan Kananan Hukumomi, Masarautun Gargajiya da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Emmanuel Umar, ya tabbatar da kashe ’yan bindigar sama da 100 tare da kwace baburansu 50 yayin farmakin.
Ya ce maharan dai na kan hanyarsu ne ta shiga garin bayan kammala harin da suka kai ofishin ’yan sanda na Nasko ranar Talata.
Aminiya ta rawaito cewa yayin harin na Nasko dai, maharan sun kashe Baturen ’Yan Sandan Yankin da wasu jami’an tsaro.