Jami’an tsaro sun gano bindigogi kirar AK-47 kimanin 150 da albarusai sama da 3,000 a gidan wani dan bindiga da suke nema ruwa a jallo a Jihar Neja.
Majiyoyi sun ce an yi dauki ba dadi tsakanin dan bindigar da jami’an tsaro na tsawon sa’o’i a daren Talata, a unguwar Gbeganu da ke Minna, babban birnin jihar, inda suka gano bindigogin da harsasai dama da 3,000.
- Yadda muka rayu a hannun mayakan Hamas —’Yar Isra’ilar da aka sako
- Ɗalibin jami’a ya ‘kashe’ Ɗan sakandare a Bauchi
Wata majiyar tsaro ta shaida wa wakilinmu cewa makaman da aka kama a gidan dan bindigar sun hada da bindigogi kirar AK-47 guda 150, bindiga kirar AA, albarusai 3,000, makamin roka, da kuma abubuwan fashewa.
Mazauna yankin sun ce sun shiga tashin hankali da jin musayawar wutar da aka fara da misalin karfe 12 na dare, kafin dan bindigar ya tsere.
Sun bayana cewa wanda ake zargin ya yi amfani da makamin roka ya rusa wani bangare na gidan nasa, inda ta nan ya samu ya tsere, amma jami’an tsaro sun kama matarsa ’ya’yansa da ke gidan.
Majiyarmu ta ce ganin jami’an tsaro ta na’urar CCTV ke da wuya, sai dan ta’addan da suka je nema ya bude musu wuta, su kuma suka mayar da martani.
Wani mazaunin unguwar ya shaida wa wakilinmu cewa, “gaskiya ba mu yi barci ba, saboda karfin karar harbe-harben, yadda ka san bom ake harbawa.
“Ta kofar gidanmu jami’an tsaron suka wuce a lokacin da za su gidan, ba mu san inda suka nufa ba, sai daga baya muka fara jin harbe-harbe.”
Ya bayyana cewa harsashi ya samu wani mai gadi a ayin musayar wutar, inda aka kai shi Asibitin Kwararru Ibrahim Badamasi Babangida domin ba shi kulawa.
A lokacin da wakilinmu ya je yankin a safiyar Talata, ya ga wasu bangayen gidan sun fadi, kofa da bango da kuma tagogin gidan kuma da ruwan harsasai a jikinsu.