Sojoji sun hallaka wasu manyan ’yan ta’adda tare da yaransu masu yawan gaske a wata arangama a Ƙaramar Hukumar Talata Mafara da ke Jihar Zamfara.
Shugabannin ’yan bindiga da suka haɗa da Auta Jijji da Dankali da Sagidi da Kachallah Rijaji da kuma Kachallah Suza sun sheƙa lahira ne a yayin musayar wuta da sojojin a ranar Alhamis.
Kakakin Birget na 1 ta Sojin Ƙasa ta Najeriya, Kyaftin Suleiman Omale, ya ce sojojin sun ƙaddamar da aikin ne bayan samun rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mai Kwanugga inda suke ta ƙone gidajen al’umma.
Ya bayyana cewa, “dakarun da ke sintiri suka yi artabu da dandazon ’yan bindiga, inda a yayin musayar wuta suka kashe shugabannin ’yan bindiga biyar da wasu da dama.”
- Yadda aka yi bikin yaye sabbin matuƙa jiragen Rundunar Sojin Saman Najeriya
- Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina
- Sarki Sanusi II ya naɗa sabon Galadiman Kano da wasu 4
Ya ƙara da cewa sojojin sun bi sawun ’yan bindigar da suka tsere inda suka ƙwato manyan bindigogi guda shida da bama-bamai da kuma harsasai iri-iri.
Washegari kuma a yayin da sojojin ke ci gaba aiki, mazauna yankin sun mika musu wasu ƙarin makaman da ’yan bindigar suka tsere suka bari.
Kyaftin Omale ya bayyana cewa fararen hula biyu sun samu raunin harbi a yayin musayar wuta amma suna samun kulawa a asibiti, a yayin da ake ci gaba a aikin gamawa da ragowar ’yan ta’addan.