✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa

Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ’yan rakiyarta shiga haramar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ta je da niyyar halartar zaman Majlasiar Dattawa…

Jami’an tsaro sun hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ’yan rakiyarta shiga haramar Majalisar Dokoki ta Kasa, inda ta je da niyyar halartar zaman Majlasiar Dattawa a ranar Talata.

Jami’an tsaro a daukacin kofofin shiga harabar majalisar sun hana ta shiga harabar majalisar ne a lokacin da ta yi yunkurin shiga domin halartar zaman ranar Talata, a yayin da magoya bayanta suka rako ta domin nuna goyon bayansu gare ta kan dakatarwar da majalisar ta yi mata.

A watan Maris ne da Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon wata shida kan zargin rashin da’a da kuma rashin bin tsarin wurin zaman da aka tanadar da mambobin majalisar a ranar 20 ga watan Fabrairu, 2025.

A kana haka ne ’yar majalisar mai wakiltar Kogit ta Tsakiya ta garzaya Babbar Kotun Abuja, wadda ta umarci majalidar ta dawo da Sanata Natasha, bisa hujjar cewa majailsar ta wuce gona da iri wajen dakatar da ita har na tsawon wata shida.

Alkalin kotu, Mai Shari’a Binta Nyako, ya bayyana cewa hukuncin da majalisar ta yanke ya yi tsauri da yawa, kuma ba shi da mazauni a doka.

Ta bayyana cewa doka na bukatar majalisar ta zauna sau 181 ne a shekara, kuma dakatarwar ta kusa tsawon wadanan kwanaki.

Ta ce hakan na nufin al’ummarta za su shafe kusan shekara guda ba tare mai wakiltans su ba a zauren majalisar, kuma ya saba da dokar kasa.

Tun loakcin Natasha ke ta kokarin komawa bakin aiki, inda a ranar Asabar ta lashi takobin halartar zama a ranar Talatar nan, idan majalisar ta dawo daga hutu.

Amma a ranar Litinin Shguaban Kwamitin Sadarwa na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu ya fitar da sanarwa yana gargadin ta da cewa ya nisanci majalsiar.

Adaramodu ya yi ikirarin cewa Natasha ba ta cika umarnin kotu na biyan tarar Naira miliyan biyar ga Gwamnatin Tarayya kan kan raina kotu ba, da kuwa wallafa sakon neman afuwa a manyan jaridu biyu da kuma shafinta na Facebook.