More Podcasts
Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam ne.
A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka.
Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa al’umma dama a kai kuma shi ne na yin kiranye ga wakilan da suka zaɓa musamman idan waɗannan wakilan basa biya musu buƙatun da suka tura su a kai.
Tuni dai al’ummar Kogi ta Tsakiya suka fara kaɗa ƙuri’un kiranye ga Sanata Natasha da suka aike ga Majalisar Dattawa bisa dalilai nasu na ƙashin kan su.
- NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci
- DAGA LARABA: Abin da doka ta ce kan dakatar da zaɓaɓɓen Gwamna
Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai tattauna ne kan matakai da sharuɗan da ake cikawa don yin kiranye ga ‘yan majalisa.
Domin sauke shirin, latsa nan