Jami’an tsaro sun kama Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, bisa zargin kisan kai da kone Sakatariyar Jam’iyyar NNPP da ke Tudun Wada a Jihar Kano lokacin da ake gudanar da zaben nan da aka kammala.
Aminiya ta ruwaito cewa ’yan sanda sun tabbatar da kisan akalla mutane uku lokacin rikicin da ya barke yayin da ake tattara sakamakon zaben Majalisar Wakilai na Doguwa/Tudunawa, wanda daga bisani aka bayyana Doguwa a matsayin wanda ya yi nasara.
- APC ta yi martani kan bukatar soke zaben ranar Asabar
- INEC ta ci gaba da tattara sakamakon zabe duk da zanga-zangar da ta barke a Abuja
Wata majiya mai tushe daga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta shaida wa wakilinmu cewa an kama Doguwa ne a Tashar Jiragen Sama ta Malam Aminu Kano lokacin da yake shirin tafiya.
Majiyar ta ce rahoton da Babban Jami’in ’Yan Sanda na Tudun Wada ya rubuta ya zargi Doguwa da jagorantar ’yan dabar da suka kona ofishin NNPP inda aka kashe akalla mutane biyu.
“Ya kuma yi amfani da bindigar dogarinsa ya harbi mutane da yawa. Don haka mun kama shi bisa zargin kisa da tayar da gobara.
“Yanzu haka yana sashen binciken masu manyan laifuffuka” a cewar babban jami’in dan sandan da ya nemi a boye sunansa.
Ko da wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai amsa wayarsa ba.
Kafin kama shi dai, Doguwa ya gana da ’yan jarida inda ya ce babu hannunsa a hayaniyar da ta faru.
Ya kuma ce ya ji labarin wai ’yan sanda na neman sa, amma ba su gayyace shi a hukumance ba.
Ya kara da cewa shi bai harbi kowa ba saboda ba shi da bindiga kuma bai san yadda ake harbi ba.
Ya ce, “ban taba rike bindiga ba. Ban ma san yadda ake rike ta ba. Kuma ban taba rike makami ba tsawon lokacin zaben nan.”
Sai dai ya ce rikicin ya faru ne lokacin da magoya bayan NNPP suka yi kokarin kona ofishin hukumar zabe yayin da magoya bayan APC su ka kore su.