Babban Kwamandan Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC), Ahmed Audi, ya ce jami’an tsaro na ba wa bata-gari bayanan sirri domin ci gaba da miyagun ayyukansu.
Audi ya ce bayanan sirri da miyagu suke samu daga jami’an tsaro da kuma fararen hula da suke hada baki da su su ne musabbabin karuwar aikata miyagun laifuka a Najeriya.
- Jirgin yakin sojoji ya hallaka masunta 20 a Borno ‘bisa kuskure’
- Daga Laraba: Wane Ne Ke Yada Labaran Karya?
“Na san za ku yarda da ni cewa ana samun karuwar aikata miyagun laifuka ne saboda jami’an tsaro da sauran al’ummomi suke taimaka wa masu aikata laifi; Saboda wajibi ne a shigo da sarakunan gargajiya da shugabannin addini da na siyasa da na matasa domin a lalubo hanyar da za a yi wa tufkar hanci,” a cewar shugaban na NSCDC.
Ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga babban taron masu ruwa da tsaki domin samar da tsaro ga kadarorin gwamnati, wanda ya gudana a Abuja ranar Talata.
Audi ya ce aikata miyagun laifuka babbar barazana ce ga kayan gwamnati, yana mai bayar da misali da jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, Borno da sauran jihohin Arewacin Najeriya.
Saboda haka ya shawarci hukumomin tsaro da su bullo da sabbi kuma nagartattun dabarun kare kayan gwamnati daga kowadanne irin masu aikata miyagun laifuka.
Ya kuma nuna damuwarsa a kan jawabin Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, wanda ya ce gwamnati tana kashe Naira biliyan 60 a duk shekara wajen gyaran bututan man fetur da bata-gari sukke fasawa a fadin Najeriya.
A don haka ya jaddada muhimmancin sauya dabaru domin samar da ingataccen tsaro ga kadarorin gwamnati daga ayyukan bata-gari.
A nasa jawabin a wurin taron, Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya ce gwamnati na kashe makudan kudade wajen samar abubuwan more rayuwa ga ’yan Najeriya.
Ya bayyana makarantu da cibiyoyin ilimi a matsayin muhimman kadarorin gwamnati da suke bukatar karin tsaro da aminci domin a samu damar koyarwa da kuma ilimi managarci.
“Gwamnati a duk matakai uku na kashe makudan kudade wajen gina abubuwan more rayuwa da za su samar ayyukan yi ga al’ummomi tare da rage talauci da inganta jin dadin rayuwar ’yan Najeriya,” inji shi.