✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an lafiya takwas sun kamu da coronavirus a rana guda

Jami’an lafiya guda takwas sun kamu da cutar coronavirus yayin gudanar da ayyukansu a ranar Laraba a jihar Bayelsa. Mutum 54 ne aka sanar sun…

Jami’an lafiya guda takwas sun kamu da cutar coronavirus yayin gudanar da ayyukansu a ranar Laraba a jihar Bayelsa.

Mutum 54 ne aka sanar sun kamu da cutar coronavirus a ranar daga cikin mutum 71 da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta yi wa gwajin a jihar ta Bayelsa.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Bayelsa Inodu Apoku, ya tabbatar da haka, ya kuma ce 11 daga cikin sabbin masu cutar sun harbu ne ta hanyar mu’amala da masu dauke da ita.

Alkaluma 54 da aka samu na cutar a ranar su ne mafi yawa na wadanda suka kamu a rana guda tun bayan bullarta a jihar, wadda yanzu ke da mutum 86 da suka kamu.