Jami’an Hukumar Kwastam ta Najeriya sun kama wani kwantaina makare da bindigogi da aka yi fasakwaurinsu daga kasar waje.
An kama kwantainar da ke dauke bindigogin ne a Tashar Jirgin Ruwa ta Tin Can Island da ke Jihar Legas, bayan mai kayan ya yi wa jami’an hukumar karya cewa talabijin din bango ne ya shigo da su Najeriya a cikin kwantainar.
- Yadda sojoji suka ragargaji Turji da yaransa a Sakkwato
- ’Yan tawayen Houthi sun kashe sojojin Sudan 14 a Yemen
Kakakin Hukumar Kwastam Reshen Tin Can, Uche Ejesieme, ya ce, “Jami’an hukumarmu sun yi nasarar kama wata kwantaina da ke dauke da makamai, tuni kuma aka killace ta sai an kammala bincike a kanta domin tabbatar da iya adadin makaman da kuma sauran muhimman bayanai.
“Yanzu haka za mu je mu yi wa kwantainar filla-filla domin mu tabbatar da iya yawan makaman da ta dauko da mutanen da ke da hannu wajen yin fasakwaurin makaman da sauran bayanan da suka dace da za mu fitar a nan gaba.”
Uche ya bayyana cewa, tun da farko sai da jami’an hukumar suka diga ayar tambaya a kan kayan da ke cikin sundukin, lura da yadda masu kula da kayan ke ta karba-karba wajen yin fitonsu.
Ya ce bayan an kammala bincike za su sanar da cikakken bayani game da miyagun makaman da aka kama ta hannun hedikwatar hukumar da ke Abuja.
“Shi ya sa ba mu fitar da sanarwa ba tukuna, sai mun tattara tuk bayanan da suka dace a game da kayan, inda suka fito da nau’ikan bindigogin. Duka wadannan za mu gano idan aka kammala bincike,” inji shi.
Hukumar ta kuma yi alkawarin yin dukkan mai yiwuwa wajen ganin an kamo duk mutanen da suke da hannu a shigo da makaman, da nufin magance matsalar fasakwaurin makamai zuwa Najeriya.