A yau Lahadi Jami’an tsaron farin kaya wato DSS sun yi nasarar ceto, wasu yara biyu da aka sace su a jihar Kebbi shekaru 3 da suka gabata.
An sace yaran ne a ranar 16 ga watan Fabrairu shekarar 2016, jami’an hukumar sun kame mutum uku da ake zargin da hannu a sace yaran wadanda suka hadar da wata mace mai suna Aghata da aka kama ta a jihar Enugu, sai Moses a jihar Anambra da Samson da aka kama shi a Legas.
Da yake mika yaran ga iyayensu da yammacin yau Lahadi, Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Atiku Bagudu, ya ce biyu daga cikin wadanda ake zargin, su ne wadanda aka kama da laifin sace yaran da aka ceto su a ranar 14 ga watan Nuwamba 2019, ya ce jami’an DSS sun sami nasarar ceto yaran a karo na biyu bayan da suka shafe sama da wata guda suna gudanar da bincike.
