Al’ummar unguwar Daneji da ke Ƙaramar Hukumar Birni a Jihar Kano na kira ga gwamnati da ta kai musu ɗauki bayan wata mesa ta ƙwace daga gidan tsohon Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris.
Mutanen wannan unguwa na zargin tsohon Akanta-Janar ɗin na kiwon dabbobi masu yawa, waɗanda daga cikisu akwai masu hatsari.
- Buhari bai taɓa girmama kowa kamar yadda Tinubu ya yi masa ba — Sani
- AGILE: ’Yan mata 40,630 za su samu tallafin karatu a Yobe
Wani daga cikin mazauna unguwar, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana yadda hankalin jama’a ya tashi sakamakon kiwon namun daji masu hatsari da ake yi a cikin gidan.
“Ni mazaunin unguwar Daneji ne. Hankalina ya tashi ƙwarai, muna cikin firgici da tashin hankali saboda an kawo zakuna muna gani, da macizai, da kada an ajiye a gidan ana kiwo,” in ji shi.
“Yanzu zancen da nake miki an samu mesa guda ɗaya ta ɓace, an nemi ta ko sama ko ƙasa a gidan ta fice ta shiga gari. Ga damina kuma. Abin akwai firgitarwa.”
Ya ƙara da cewa akwai: “Akwai ’ya’yan zakuna guda biyu a cikin gidan, ta baya aka musu keji. A kan idon mutanen unguwa ake yanka musu shanu ana ba su, suna ci.
“Sai kuma aka kawo macizai kala-kala wajen guda 10 a ka saka su a irin bokitin roba ɗin nan da ake iya ganin cikinsu.
Ya ce mesar da ta tsere, an yi mata wani irin gida na gilas, amma abun mamaki ta ɓace ba a san inda ta shiga ba.
“Sai ita kuma mesar, an sakata a cikin gidan gilas. Daga baya sai aka kawo kada guda biyu da kunkuru. Ba ɓoyayyen abu ba ne domin an ce yana kai baƙinsa su kalli dabbobin.”
Ya jaddada hatsarin da ke tattare da wannan lamari, inda ya nemi ɗaukin masu ruwa da tsaki.
“To yanzu dai mesar ta ƙwace tun shekaran jiya (Alhamis) ta shiga unguwa, ba a gano ta ba.
“Ga yanayin damina, ga yara na ta yawo a unguwa, ba a san me zai faru ba. Kin ga dole hankalinmu ya tashi.”
Aminiya ta tuntuɓi mai unguwar Daneji, Malam Abba Lawan, kan lamarin, kuma ya tabbatar da cewar yana ɗaukar matakin da ya dace.
Ya bayyana wa Aminiya cewa: “Mun yi magana da shi (mai gidan), ya kuma yi alƙawarin ɗauke dabbobin duka saboda ba zai yiwu a ce dabbobi masu hatsari na rayuwa kusa da al’umma ba.
“Dabbobin nan fa suna da wayo duk da ba mutane ba ne. A haka ita ma mesar ta samu hanya ta zurare.”
Ya kara da cewa: “Yanzu dai ya tabbatar min cewa ya yi magana da waɗanda suka kawo masa dabbobin kuma suna nan suna ƙoƙarin samo ta.
“Amma ni a raina na gindaya iya wa’adin da na bashi. Idan ya saɓa, zan miƙa zancen ga hukumar ’yan sanda.”
Har yanzu dai al’ummar Daneji na cikin firgici saboda ɓatan dabo da wannan mesa ta yi a cikin unguwar.
Suna fatan gwamnati za ta hanzarta ɗaukar mataki don kare lafiyarsu, musamman ganin cewa damina na ci gaba da sauka.