Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ayyana sunayen mutum 41 da zai nada a matsayin kananan jakadun Najeriya zuwa kashen waje.
Hakan na kunshe ne a takardar da Shugaban Kasa ya aike wa Majalisar Dattawa na neman amincewarta da mutanen da kuma karin mutum daya da zai nada babban jakada daga Birnin Tarayya.
Shugaban Majisar Dattaawa Ahmed Lawan ya bayyana hakan yayin karanta sakon a zaman majalisar na ranar Laraba, makonni kadan bayan amincewar majalisar da sunayen wasu mutum 42 da shugaban ya nada manyan jakadu.
Buharin na kuma neman amincewar ‘yan majalisar da sunan Suleiman Sani a matsayin sabon babban jakadan Najeriya.
Ga jerin sunayen mutanen da aka gabatar da kuma jihohin da suka fito:
—————————————————————————
- Injiya Umar Suleiman (Adamawa)
- L.S. Mandama (Adamawa)
- Oboro Effiong Akpabio (Akwa Ibom)
- Chief Elejah Onyeagba (Anambra)
- Abubakar D. Ibrahim Siyi (Bauchi)
- Philip K. Ikurusi (Bayelsa)
- Hon. Tarzcor Terhemen (Binuwai)
- Paul Oga Adikwu (Binuwai)
- Al-Bishir Ibrahim Al-Hussain (Borno)
- Brig Janar Bwala Yusuf Bukar (Borno)
- Farfesa Monique Ekpong (Cross River)
—————————————————————————
- Oma Djebah (Delta)
- Ominyi N. Eze, Ebonyi (Ebonyi)
- Yamah Mohammed Musa (Edo)
- Manajo Janar C. O. Ugwu (Inugu)
- Dakta Hajara I. Salim (Gombe)
- Obiezu Ijeoma Chinyerem (Imo)
- Ali M. Magashi (Jigawa)
- Farfesa M. A. Makarfi (Kaduna)
- Hamisu Umar Takalmawa (Kano)
- Imam Galandanci (Kano)
—————————————————————————
- Amina Ado Kurawa (Kano)
- Amb. Yahaya Lawal (Katsina)
- Dare Sunday Awoniyi (Kogi)
- Ibrahim Kayode Laaro (Kwara)
- Abioye Bello (Kwara)
- Zara Maazu Umar (Kwara)
- Ademola Seriki (Lagos)
- Henry John Omaku (Nasarawa)
- Cif Sarafa Tunji Ishola (Ogun)
- Misis Nimi Akinkube (Ondo)
—————————————————————————
- Adejaba Bello (Osun)
- Adeshina Alege (Oyo)
- Debo Adesina (Oyo)
- Folakemi Akinyele (Oyo)
- Shehu Abdullahi Yibaikwai (Filato)
- Hon. Maureen Tamuno (Ribas)
- Faruk Yabo (Sokoto)
- Adamu M. Hassan (Taraba)
- Alhaji Yusuf Mohammed (Yobe)
- Abubakar Moriki (Zamfara).