Allah Ya yi wa Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Mai Shari’a Sylvanus Adiewere Nsofor rasuwa.
Jakadan na Najeriyan ya rasu ne yana da shekara 85 a wani asibiti da ke yankin Maryland na kasar Amurka ranar Alhamis da dare.
- N-Power da GEEP: An kara yawan masu samu zuwa miliyan daya-daya
- Yadda rashin tsaro ya sa ’yan Arewa dawowa daga rakiyar Buhari
- Yadda Kanawa 16 suka mutu a hatsarin mota a Kaduna
A ranar 12 ga watan Nuwamban 2017 ne Mai Shari’a Sylvanus Nsofor ya fara aiki a matsayin Jakadan Najeriya a Amurka, har zuwa lokacin da ya koma ga Mahaliccinsa.
Ya samu mukamin ne bayan rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a Amurka, Farfesa Adebowale Adefuye, wanda ya mutu dab da karewar wa’adinsa.
Mamacin shi tsohon Alkali ne a Kotun Daukaka Kara ta Najeriya.
An haife shi ne a ranar 17 ga Maris, 1935 a Oguta, Jihar Imo, kuma tsohon dalibin tsohuwar Kwalejin Aikin Lauya ta Holbor da ke birnin London na kasar Birtaniya ne.
A kwalejin ya samu digirinsa na farko a 1962 kafin ya samu digirinsa na biyu a 1964 daga Kwalejin Tattalin Arziki ta London.