Assalamu Alaikum Edita. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Don Allah ka ba mu da ma a wannan sabuwar shekarar ta 01-01-2018 In yi ja je a kan abubuwan da suka faru a kasata Najeriya, musanman ma a yankin Arewa Maso Gabas, kan hare-haren kungiyar Boko Haram da ya yi sanadiyar rasa rayukan al’umma da dama a shekarar 2017. Hakika munyi rashin ‘yan uwan mu sosai a wannan 2017 yanki na Arewa maso Gabas, inda mata da dama suka zama zawarawa yara kanana suka zama marayu. Abin tausayi sansanonin ‘yan gudun hijira cike da mata da kananan yara a gaskiya akwai tausayi idan mutum ya ga yadda wadannan bayin Allah ke rayuwa cikin kuncin da wahala yunwa na kashe mutanen boko haram, na tayar da hankalin jama’a. Sojoji na iyakar kokarin su wajen kare rayukan al’umma sai dai babu kayan aiki ga sojoji. Idan kuma na komo yankin Arewa maso Yamma nan ma barayin shanu sun yi yawa ‘yan ta’adda sun kashe jama’a a Zamfara, ana sace mutane a Jihar Kaduna. Abin sai dai addu’a a karshe nake addu’ar Allah ya kawo mana zaman lafiya a kasar mu Najeriya dama duniya baki daya.
Amin 08067873852. Arabiyyu Muhammad Gidan Madi A Jihar Sakkwaton Najeriya. Arabiyyu Muhammadgmd [email protected]