Tsohuwar Sakatariyar jin daɗin jama’a a jam’iyyar APC reshen jihar Legas, ta rasu.
Bankole, ɗaya daga cikin jiga-jigan mata ta APC a Legas daga yankin Epe, ta rasu ne a yayin da take gudanar da aikin Hajji hajji a kasar Saudiyya.
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar a jihar, Mista Seye Oladeje, ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis cewa, marigayiya Bankole ta kasance jajirtacciya ’yar jam’iyyar.
“Mutuwarta ta taba zukatanmu da ban takaici. Ta kasance jagorar jam’iyya mai jajircewa kuma ƙwararriya.
- Sojoji za su sayo jirage 50 domin yaƙi da ta’addanci a Arewa
- Gwamnatin Kano ta ba da umarnin fitar da Sarki Bayero daga Fadar Nassarawa
“Marigayiyar ta kasance ƙwararriya mai wayar da kan jama’a da zaburarwa ga mata don shiga harkokin siyasa. Allah Ya jikan ta da rahama,” in ji Oladejo.
Kamfanin NAN ta ruwaito cewa Shugabar Karamar Hukumar Epe, Madam Surah Animashaun, a ranar Alhamis ta tabbatar da mutuwar Bankole.
Animashaun, a cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce marigayiyar ta kasance mai hazaƙa kafin ta bar ƙasar zuwa aikin Hajji.