✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jadawalin kwata-final na Gasar Zakarun Turai

Za a buga wasan karshe na Champions League a filin Wembley ranar Asabar 1 ga watan Yuni.

Kawo yanzu kungiyoyi takwas ne za su ci gaba da Gasar Zakarun Turai ta Champions League da Europa League na bana a zagayen kwana-final.

An dai raba jadawalin ci gaba da zagayen na gaba a wannan Juma’ar a birnin Nyon na Switzerland.

Yayin fitar da jadawalin, babu maganar fifita wata kungiya kan kwazonta, kuma kungiyoyi daga kasa daya za su iya fuskantar juna a fafatawar da za a yi gida da waje a zagaye na kwata fainal.

Ana sa ran buga wasan karshe na Champions League a filin Wembley ranar Asabar 1 ga watan Yuni.

Ga dai yadda jadawalin kwata-final na Champions League ya kaya:

Arsenal v Bayern Munich

Atletico Madrid v Dortmund

Real Madrid v Manchester City

Paris St-Germain v Barcelona

Ga kuma jadawalin Europa League:

AC Milan v Roma

Bayer Leverkusen v West Ham

Benfica v Marseille

Liverpool v Atalanta

Za a yi karawar farko ta Europa League a ranar 11 ga watan Afrilu inda karawa ta biyu kuma za a yi a ranar 18 ga watan na Afrilu.

A ranar 2 ga watan Mayu za a buga wasan zagayen kusa da ƙarshe, sai kuma wasa na biyu na zagayen kusa da ƙarshe a ranar 9 ga watan Mayu.