✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Izala za ta yi wa nakasassu hannuwa da kafafu na zamani

kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), za ta yi wa nakasassu hannuwa da kafafu na zamani don su samu damar tafiya ko yin…

kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), za ta yi wa nakasassu hannuwa da kafafu na zamani don su samu damar tafiya ko yin aiki cikin sauki. 

Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya yi wannan alkawarin a lokacin da yake jawabi yayin taron kara wa juna sani na kwana uku da kungiyar ta shirya wa ’yan agajin Abuja.
Taron wanda aka kammala shi a ranar Lahadin makon jiya, an shirya shi ne a babbar sakatariyar kungiyar da ke Abuja don yi wa ’yan agajin bitar muhimman abubuwa da suka shafi aikin taimakon farko a yayin aikinsu.
An shirya bada tallafi ga nakasassun ne a karkarshin asusun ‘Manara’ da kungiyar ta kaddamar shekara biyu da ta gabata, wadda ta rika tallafa wa marayu da gajiyayyu ciki har da ’yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu.
“Mun kaddamar da wannan kwamiti ne wanda zai rika kula da bayar da tallafi ga nakasassu da suka rasa hannuwa da kafafunsu a karkarshin Mataimakin Daraktan Agaji na kasa, Alhaji Abdullahi Digi, kwamitin zai fara aikin zakulo nakassun daga ko’ina a fadin kasar nan don yi musu kafafu da hannuwa na zamani don su rika walwala tare yin ayyuka da kafafu da hannuwa kamar kowa. Don haka duk wadanda suke da matsalar rashin kafa ko hannu, ina yi musu albishir da cewa su je kai tsaye zuwa ofisoshinmu, mun tanadi kwararru wadanda nan ba da jimawa ba za su fara aikin samar musu da hannuwa da kafafun, musamman wadanda rikicin Arewa maso Gabas ya shafa.
Ya bayyana aiki ne na jin kai wadda ya game Musulmi da Kirista ba tare da nuna bambanci ga kowa ba.
Shugaban ya ja hankalin ’yan agajin su ci gaba da yin aiki da dukkan darussan da shugabanni suka karantar da su a yayin wannan bita, sannan su sanya ido kan zabukan da ke tafe.